'Yan bindiga sun yi awon gaba da ma'aikata 6 daga wurin haƙar ma'adinai a Kogi

'Yan bindiga sun yi awon gaba da ma'aikata 6 daga wurin haƙar ma'adinai a Kogi

  • Yan bindiga dauke da miyagun makamai sunyi garkuwa da ma'aikatan wani kamfanin tangaran shida a Emiworo dake Ajoakuta a Jihar Kogi
  • Mai magana da yawun yan sandan Jihar Kogi ya tabbatar da faruwar lamarin kuma ya bayyana cewa ba zasu yi kasa gwiwa ba don ceto ma'aikatan
  • Matar daya daga cikin ma'aikatan ta ce a rude take kuma bata san yadda zata yi ba, jami'an tsaro su taimaka su ceto su

'Yan bindiga sunyi garkuwa da ma'aikata shida na wani kamfanin kera tangaran da ke Itobe a Jihar Kogi kamar yadda The Cable ta ruwaito.

The Guardian ta ruwaito cewa William Aya, mai magana da yawun yan sandar Jihar Kogi, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata tattaunawa da yan jaridu a Lokoja, babban birnin jihar, ranar Laraba.

Taswirar Jihar Kogi
Taswirar Jihar Kogi. Hoto: Channels TV
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Masu Riƙe Da Muƙaman Siyasa a Kebbi Sun Sadaukar Da Rabin Albashinsu Don Yaƙar Ƴan Bindiga

Da yake bayyana cewa anyi garkuwa da ma'aikatan ranar 29 ga watan Yuni, ya kara da cewa ma'aikatan na aiki ne a daya daga cikin wajen hakar ma'adanai na kamfanin a Unguwar Emiworo da ke karamar hukumar Ajaokuta, lokacin da aka yi garkuwa da su.

Sai dai, Aya, ya bayyana cewa yan sanda ba su samu rahoto ba sai da safiyar Laraba.

Ya ce sun samu rahoton yan bindigar na dauke da miyagun makamai, kuma sun mamayi ma'aikatan kafin su kora su daji.

Mai magana da yawun yan sandan ya kara da cewa rundunar yan sanda tana aiki tare da hadin gwiwar sauran jami'an tsaro don ceto wanda abun ya shafa, ya na mai bayyana cewa tuni sun fara farautar yan bindigar.

KU KARANTA: Sunday Igboho ya nemi alfarma daga wurin Rundunar 'Yan Sanda gabanin gangamin Legas

Ya tabbatarwa iyalan wanda abun ya shafa cewa jami'an tsaro zasu yi kokarin tabbatar da an ceto ma'aikatan cikin koshin lafiya.

Matar daya daga cikin wadanda aka sace ta roki yan sanda su ceto su

A daya bangaren, Asanah Shaibu, wanda mijin ta, Hassan, yana cikin wanda aka sace ta roki yan sanda da su ceto mijin ta cikin koshin lafiya hade da sauran wanda aka dauke.

Ta shaida wa jaridar cewa:

"Eh, miji na yana cikin ma'aikatan tangaran da aka yi garkuwa dasu a Emiworo. Bamu ji komai daga wajen barayin ba. Maganar da nake ma yanzu a rude nake kuma bansan inda zan nufa ba."

Mafarauta sun ɗirkawa mai garkuwa harsashi ya mutu wurin karɓar kuɗin fansa

A wani rahoton daban, mafarauta sun harbe wani mutum da ke cikin gungun masu garkuwa da mutane uku har lahira yayin da ya tafi karbar kudin fansa a kauyen Abobo a karamar hukumar Okehi na jihar Kogi, Daily Trust ta ruwaito.

Wani mafarauci da ke cikin wadanda suka shirya atisayen, ya ce an yi harbin ne misalin karfe 5.23 na asubahi a ranar Talata.

Mutumin ya fito ne daga wurin da ya ke boye a yankin Abobo, bayan Itakpe, wasu yan kilomita kadan daga babban titi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel