Kowa zai gujewa Buhari kafin 2019 - Buba Galadima

Kowa zai gujewa Buhari kafin 2019 - Buba Galadima

Cikin watanni 18 da kafuwar jam'iyyar APC bisa kan gadon mulkin Nijeriya rigingimu suke ta barkewa a cikinta tun ma ba na musayar kalamai ba a tsalanin jigajigan jam'iyyar, musamman talsakanin Tinubu da Oyegun da kuma tsakanin El-Rufai da Atiku da kuma tsakanin El-Rufai sa Sanata Shehu Sani dai sauran rigingimu a tsakaninsu makamantan haka.

Kowa zai gujewa Buhari kafin 2019 - Buba Galadima
Shugaba Buhari

Wannan ne ya haifar da cece kuce a cikin jam'iyyar inda wasu ke ganin ya kamata a sake ba Shugaban Kasa Buhari damar sake tsayawa takara a jam'iyyar ba tare da hammaya ba, wasu kuwa irin su Buba Galadima wanda yai aiki tare da Shugaban Kasa Bukharin a siyasar adawa tun a takarar shekarar 2003 da 2007 da ta 2011 har zuwa ta 2015 ke ganin ba ta sabau bindiga a ruwa a ce wai Buharin zai sake fitowa takara a jam'iyyar APC a matsayin dan takarar jam'iyyar a 2019 ta irin nuna halin ko inkula da kuma rikon sakainar kashin da yake yi wa uwar jam'iyyar, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito mana.

KU KARANTA: An gano wadda tafi kowa tsufa a Najeriya (Hotuna)

Galadima ya bayyana cewa jam'iyyar APC a yanzun ta zama kamar marainiya wajen rashin samun uba daya kwakkwara da zai iya tsawatawa wajen kashe duk wata fitinar da ta fito a cikinta.

Haka kuma majiyar tamu ta kara rawaito mana cewa Buba Galadima ya kuma bayyana Buhari a matsayin wanda ke nuna ko'in kula wajen kare manufofi da martabobojin jam'iyyar , musamman wajen kashe duk wata wutar rikicin da ta fito a cikinta, wanda hakan na iya haifar wa Buharin rashin tudun dafawa a zaben dake gaba na 2019.

&feature=youtu.be

Asali: Legit.ng

Online view pixel