Don Allah ka nada ni shugaban hukumar INEC – Injiniya Buba Galadima ga Buhari
Tsohon aminin shugaban kasa Muhammadu Buhari, kuma tsohon sakataren jam’iyyar CPC, Alhaji Buba Galadima ya roki shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada shi shugaban hukumar zabe mai zaman kanta, INEC.
Jaridar Blueprint ta ruwaito Buba Galadima ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da gidan jaridar Daily Independent, inda yace idan har shugaba Buhari ya cika masa burinsa, ba zai bukaci kudi daga gwamnatin tarayya kafin ya shirya zabe ba.
KU KARANTA: Yadda Dasuki ya yi amfani da Sojojin haya daga kasashen wajen murkushe Boko Haram
Galadima ya bayyana haka ne yayin da yake caccakar shugaban hukumar mai ci, Farfesa Mahmud Yakubu, inda ya zarge shi da hada kai da hukumomin tsaro wajen kayar da jam’iyyar PDP a zaben shekarar 2019.
“Ba mu bukatar gwamnati ta dinga kashe kudinta wajen shirya zabe, saboda zamu iya rokon kungiyoyi da hukumomi masu bayar da tallafin su kawo mana kayan aiki, kuma su biya ma’aikatan zaben, a haka zamu samu hukumar zabe mai cin gashin kanta.
“Idan ba za su iya yin haka ba, toh su nada ni shugaban INEC su gani, ni zan samo kudaden da ake bukata domin gudanar da zabe, b azan tambayi gwamnati ko kwabo ba, bamu bukatar wani jami’in tsaro ya sanya idanu a kan zaben.” Inji shi.
A wani labarin kuma, rahotanni sun bayyana wani jigoa tsakanin shuwagabannin jam’iyyar APC mai mulki zai shirya zanga zangar neman an ture Kwamared Adams Oshiomole a matsayin shuhgaban jam’iyyar.
Jigon mai suna Kabiru Adjoto ya bayyana cewa gudanar da wannan gangamin zanga zangar ne a farkon shekarar 2020 domin bayyana bacin ransa da salon kamun ludayin mulkin Oshiomole, wanda yace ya janyo rarrabuwai kai a cikin jam’iyyar.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng