Waiwaye: Lokacin da gwamnan Zamfara yace idan yayi niyyar cutar da PDP kada Allah ya bashi abinda yake so
- Hausawa suka ce waiwaye adon tafiya
- Gwamnan Zamfara a 2019 da ya hau mulki yayi rantsuwa bashi da niyyar cutar da PDP
- Shekaru biyu bayan haka, jam'iyyar PDP tace ya yi mata butulci
Gwamna Bello Matawalle ya sauya sheka daga Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zuwa Jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
A wani taron gangami da aka shirya wa gwamnan na Zamfara a Gusau, babban birnin jihar, a ranar Talata, Mai Mala Buni, gwamnan Yobe kuma shugaban kwamitin riko na APC ya gabatar da tutar APC ga Matawalle.
Matawalle, wanda ya nuna farin cikinsa da yadda aka karbe shi a cikin jam'iyyar, ya yi kira ga hadin kai tsakanin masu ruwa da tsaki don bunkasa jihar.
Ya ce:
“Daga yau, Ni, Bello Matawallen Maradun, gwamnan Zamfara, ina mai farin cikin sanar da ficewata daga PDP zuwa APC. Daga yau, Ni cikakken dan APC ne kuma shugaban APC a Zamfara.
DUBA NAN: Najeriya ce kan gaba a yaran da ba sa zuwa makaranta a yankin Sahara - Ministan Ilimi
DUBA NAN: Ina PDP, ba zan yi butulci ba, ba zan koma APC ba: Mataimakin gwamnan Zamfara
Amma a 2019, gwamnan ya lashi takobin cewa ba shi da niyya na cutar da jam'iyyar PDP. Kuma yace kada Allah ya bashi abinda yake so idan yayi hakan.
A wani bidiyo da ya yadu a kafafen ra'ayi da sada zumunta, Matawalle yace:
"Ina ranstuwa da Allah. Zan yi wannan tafiyar tsakanina da Allah. Idan ina da wata niyya ta cutar da wani a nan ko jam'iyyarmu ta PDP, kada Allah ya bani abinda nike so duniya da lahira."
Kalli bidiyon:
Ina PDP, ba zan koma APC ba: Mataimakin gwamnan Zamfara
Mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Muhammad Gusau, ya lashi takobin cewa zai cigaba da zama a jam'iyyar People’s Democratic Party PDP, duk da cewa gwamnan jihar, Bello Matwalle ya koma All Progressives Congress APC.
Dukkan Sanatocin Zamfara uku, yan majalisar wakilai shida da yan majalisa jiha 24 sun sauya sheka tare da gwamnan illa mataimakinsa.
Muhammad Gusau ya ce zai cigaba da kasancewa da PDP saboda jama'ar PDP suka tsaya da su lokacin da suke cikin bukata, rahoton Daily Trust.
Asali: Legit.ng