Najeriya ce kan gaba a yaran da ba sa zuwa makaranta a yankin Sahara - Ministan Ilimi

Najeriya ce kan gaba a yaran da ba sa zuwa makaranta a yankin Sahara - Ministan Ilimi

  • Karamin Ministan Ilimi ya ce Najeriya nada yara fiye da miliyan 10 da ke gararamba kan titi ba sa zuwa makaranta
  • Ya nuna yadda ake da gibin karancin kwararrun malamai a makarantun kasar nan
  • Sai dai ya jinjina wa Gwamnan Jihar Katsina game da yadda ya inganta ilimi a jiharsa

Karamin Ministan Ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba, ya ce Najeriya ita ce kan gaba a yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a yankin Kudu da Hamadar Sahara.

Mista Nwajiuba ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da shirin “Samar wa kowa nagartaccen ilimi (BESDA)”, da aka gudanar a Katsina ranar Litinin.

Ya ce Najeriya tana da adadin yaran da ba sa zuwa makarantun da aka kiyasta sun kai 10,193,918.

A cewarsa,

“Kalubalen da ke tattare da bangaren ilimi a Najeriya ya nuna da akwai wagagen gibin da ya kamata a cike. Sashen ilimin na cike da matsalar jahilci da lalacewar sha’anin koyarwar da ma makarantun.”
“Muna fuskantar matsalar karancin kwararrun malamai da na lalacewar makarantun da kayayyakin koyarwa da ma rashin samar wa bangaren Isa’s sun kudaden gudanarwa,” kamar yadda ya fada.

DUBA NAN: Ina PDP, ba zan yi butulci ba, ba zan koma APC ba: Mataimakin gwamnan Zamfara

Najeriya ce a gaba wajen yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a yankin Sahara
Najeriya ce kan gaba a yaran da ba sa zuwa makaranta a yankin Sahara - Ministan Ilimi @Twitter
Asali: Twitter

KU KARANTA: Wata mata tana neman mutumin da ta aura a dandalin taron dalibai tun lokacin suna firamare

Ya jinjinawa gwamnan jihar Katsina

Ministan ya taya gwamnan Jihar Katsina, Aminu Masari, murna kan nasarorin da ya cimma wa a bangaren inganta ilimi a jihar, Premium Times ta ruwaito.

Ya ce,

“wannan ya nuna ingantaccen shugabanci da kudurin gwamnan ta fuskar ilimi da ma jarabarsa ta ganin ya inganta bangaren ilimi wanda shi ne babban jari ga jihar.”

Ministan ya ce shirin na BESDA ya mayar da hankali ne a jihohi 17; 13 daga ciki jihohin Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas ne tare da jihohin Neja da Oyo da Ebonyi da Ribas.

A nasa tsokacin, Gwamna Aminu Bello Masari ya jinjina wa mai’aikatar ilimi ta tarayya da shirin samar da ilimin bai daya “kan hangen nesan da suka nuna wajen kirkiro da shirye-shirye masu ma’ana domin inganta bangaren ilimi da kuma ci gaban jama’a baki daya.”

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng