‘Yanuwa sun yi karo-karo sun hada N2m, Sarkin da aka yi garkuwa da shi, ya samu 'yanci

‘Yanuwa sun yi karo-karo sun hada N2m, Sarkin da aka yi garkuwa da shi, ya samu 'yanci

  • Sarkin Eda-Ilen da aka yi awon-gaba da shi ya fito daga hannun ‘Yan bindiga
  • ‘Yanuwa ne su ka hada miliyan biyu da aka biya domin a kubuto da Basarake
  • Ana tunani an tsare Sarkin ne a jejin da ke tsakanin Ode Ekiti da Agbado Ekiti

Rahoton da mu ka samu daga Punch ya ce wadanda suka sace Eleda na kasar Eda-Ile, a karamar hukumar Ekiti ta gabas, jihar Ekiti, sun fito da shi.

Mai martaba Oba Benjamin Oso ya samu ‘yanci daga hannun masu garkuwa da mutane bayan ya shafe kwanaki uku a tsare wajen miyagun ‘yan bindiga.

An bukaci a kawo Naira miliyan 20

‘Yan bindigan da suka yi awon-gaba da mai martaban sun tuntubi ‘yanuwansa, inda su ka bukaci a biya su kudi har Naira miliyan 20 kafin su fito da shi.

KU KARANTA: An kashe wani Dalibi wajen zanga-zanga a Kaduna

Bayan ‘yanuwan Basaraken sun yi ta tattauna wa da wadannan mutane, sun rage kudin da suka bukata. 'Yanuwan sun ce ba su da dalilin Naira miliyan 20.

Wani daga cikin ‘yanuwan Cif Benjamin Oso ya shaida wa manema labarai cewa Mai martaban ya fito a jiya bayan an samu an bada Naira miliyan biyu.

‘Dan uwan Basaraken da ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce an kai kudin a ranar Lahadi da daddare, sai ga Oba Benjamin Oso ya dawo gida ranar Litinin.

“Kabiyesi ya samu ‘yanci a ranar Lahadi cikin dare, bayan ‘yan bindigan sun sake shi. ‘Yanuwa sun biya Naira miliyan biyu a cikin N20m da aka nema.”
Jami'an tsaro Hoto: www.dw.com/en
Wasu jami'an tsaro su na bakin aiki Hoto: www.dw.com/en
Asali: UGC

KU KARANTA: Sojoji sun kashe Boko Haram 12, an rasa Sojoji 2 a wani hari

“Mutane da dama ne suka taru, su ka hada wannan kudi da aka biya domin kubutar da shi.”
“Yanzu haka da na ke yin magana da kai ya na kwance a wani shahararren asibitin kudi da ke babban birnin jihar Ekiti, Ado-Ekiti, inda ake duba lafiyarsa.”

Jami'an tsaro sun yi magana

Jami’in da ke magana da bakin ‘yan sanda na Ekiti, Sunday Abutu, ya tabbatar da wannan labari, ya ce dakarun ‘yan sanda sun yi kokarin kubuto da Basaraken.

Kun tuna wannan Bawan Allah mai sarautar gargajiya ya fada hannun masu garkuwa da mutane ne a ranar Juma’a, 25 ga watan Yuni, 2021, a hanyar zuwa gona.

Jami’an tsaro sun ce an tsare Sarkin ne a jejin da ke tsakanin Ode Ekiti da Agbado Ekiti a jihar Ekiti. Rundunar 'Yan sandan ba su yi nasarar kubutar da shi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng