Rashin tsaro: Gwamnatin Ingila za ta kashe fiye da Naira Biliyan 1 wajen yakar Boko Haram

Rashin tsaro: Gwamnatin Ingila za ta kashe fiye da Naira Biliyan 1 wajen yakar Boko Haram

  • Gwamnatin kasar Birtaniya za ta taimaka wajen yaki da ‘Yan ta’addan ISWAP
  • Ministocin kasashen waje sun yi wani zama a Italiya, suka dauki wannan mataki
  • Za a ba yankin Chadi gudumuwar kudi domin kawo karshen irinsu Boko Haram

Kasar Birtaniya ta ce ta shirya kashe kudi har fam miliyan £2.16m da nufin ba Najeriya da sauran kasashen da ta ke makwabtaka da ita gudumuwa.

The Nation ta ce Ministan harkokin kasar wajen Birtaniya, Dominic Raab, ya bayyana wannan da yake magana a ranar Litinin, 28 ga watan Yuni, 2021.

Dominic Raab yake cewa Ingila za ta taimaka domin ganin an yi maganin ‘yan ta’addan kungiyoyin Boko Haram da ISWAP da su ke ta’adi.

KU KARANTA: Sojoji sun hallaka 'Yan ta'addan Boko Haram a Borno

Sauran kasashen yankin Chadi da za su amfana da wannan gudumuwa su ne Kamaru, Nijar da Chadi.

Jaridar ta ce Ministan kasar Turan ya yi wannan albishir a wajen taron da aka yi da Ministocin harkokin wajen kasashe 45 a birnin Rome, kasar Italiya.

Ministocin sun bayyana cewa za a fitar da wadannan makudan kudi saboda barazanar da yankin nahiyar Afrika ta yamma ke fuskanta daga ‘yan ta’adda.

Ministocin kasashen ketaren sun yi wannan zama a karkashin inuwar Global Coalition Against Daesh/ISIS da aka kafa domin a kawo karshen ta’addanci.

Rashin tsaro: Gwamnatin Ingila za ta kashe fiye da Naira Biliyan 1 wajen yakar Boko Haram
Muhammadu Buhari da Boris Johnson Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

KU KARANTA: ‘Yan Majalisa sun ce an yi barnar N84bn a NSITF

Rahoton ya ce taron ya kunshi yadda kasashen za su kara hada-kai su yaki kungiyoyin ta’adda irin ISIS da takwarorinsu da su ke hallaka mutane a Afrika.

“Wannan zai bada gudumuwa wajen kokarin da mu ke yi na mafani da sojoji wajen karya ISIS da sauran kungiyoyi, da karya kwarin gwiwar ‘yan ta’adda.”
“Shekaru biyu da ganin bayan ISIS a Iraki da Siriya, har yanzu barazanarsu na nan. Abin takaici, ana samun yaduwarsu a Afrika, shiyasa mu ke hada-kai.”

A makon jiya ne aka ji cewa an yi arkuwa da wani Basarake a jihar Ekiti. A halin yanzu, Mai martaba ya bar hannun ‘Yan bindiga, ya na kwance a gadon asibiti.

'Yan sanda sun ce Mai martaba Oba Benjamin Oso ya samu ‘yanci daga hannun masu garkuwa da mutane bayan ya shafe kusan kwanaki uku a tsare wajen ‘yan bindiga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel