Shugaba Buhari ne kadai ba barawo ba a Najeriya – Lauretta Onochie
- Onochie tace su Janar Babangida da Abacha da Abdussalami duk barayi ne
- A cewar ta Shugaba Buhari ne kadai ba a samu da laifin sata a Gwamnati ba
- Don haka tace irin su Obasanjo ke gudun Shugaban ya sake tsayawa takara
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ne kurum zakka a jerin tsoffafin Shugannin kasar nan wajen satar kudin al’umma a lokacin da su ke kan mulki inji wata Hadimar sa Lauretta Onochie.
Lauretta Onochie wanda tana cikin masu ba Shugaban kasar shawara a kafafen sada zumunta na zamani ta bayyana wannan ne a shafin ta na Tuwita kwanan nan. Onochie ta fitar da wani hoto na tsofaffin Shugabannin kasar tace duk manyan barayi ne.
KU KARANTA: Obasanjo bai isa ya hana Buhari takara ba – Inji Jam’iyyar APC
Akwai irin su tsohon Shugaban kasa Janar Ibrahim Babangida da kuma Marigayi Janar Sani Abacha da Abdulsalami Abubakar a jerin. Haka kuma akwai Shugabannin da su ka mulki kasar a farar hula irin su Goodluck Jonathan, da Olusegun Obasanjo.
A cewar ta, Duniya ta yarda cewa Shugaba Buhari ne kadai ba a taba zargi da laifin satar dukiyar Jama’a ba don haka irin su tsohon Shugaban kasa Obasanjo su ke kiran Shugaba Buhari da ya hakura da tsayawa takara a zabe mai zuwa na 2019.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng