Shugaban PDP ya bayyana abin da ya sa APC ta ke karbe mata Gwamnoni daya-bayan-daya
- PDP ta yi Allah-wadai da dauke mata Gwamnoni da Jam’iyyar APC ta ke yi
- Shugaban PDP na kasa baki daya, Prince Uche Secondus, ya fito ya yi magana
- Uche Secondus ya ce rasa Gwamnonin da su ke yi ba zai hana su cin zabe ba
Jaridar Punch ta fitar da rahoto cewa jam’iyyar PDP ta yi magana game da sauya-shekar da wasu gwamnonin jihohi su ke yi zuwa APC mai mulki.
Dole ake yi wa Gwamnonin PDP su shiga APC
Shugaban jam’iyyar PDP mai adawa, ya zargi gwamnatin tarayya da tursasa wa gwamnonin da aka zaba a karkashin PDP, su koma jam’iyyar APC.
Prince Uche Secondus ya yi wannan jawabi a garin Abuja a ranar Talata, 29 ga watan Yuni, 2021, bayan ya kira wani taron manema labarai da yamma.
KU KARANTA: Yari ya bi Bello Matawalle a matsayin sabon Jagoran APC a Zamfara
A cewar Prince Uche Secondus, babu abin da jam’iyyar APC ta tabuka a shekaru shida kan mulki, don haka ne ta ke murnar jawo gwamnonin hamayya.
PM News ta rahoto Uche Secondus, a matsayinsa na shugaban PDP na kasa ya na gunaguni.
“Abin kunya ne ga gwamnonin da duk suka bar PDP saboda tsoro. An yi masu barazana ne ta hanyar amfani da karfin gwamnati (ta tarayya).”
“Amma ina farin ciki da cewa talakawan da suke tare da mu, musamman a Zamfara, ba su bar mu.”
KU KARANTA: Ba zan bi Matawalle ba - Mataimakin Gwamnan Zamfara
“Bisa dukkan alamu, gwamna Bello Matawalle ya manta yadda ya zama gwamnan jihar Zamfara, ya na bukatar a tuna masa bai isa ya koma wata jam’iyya da kuri’un da PDP ta ba shi a lokacin zabe ba.”
Babu matsala don wani Gwamna ya bar PDP
Bayan haka, shugaban jam’iyyar hamayyar ya ce talakawa sun gaji da mulkin gwamnatin APC, saboda haka duk da yawan gwamnonin da PDP ta rasa, za ta ci zabe.
“Su na bin gwamnoni, mu kuma talakawan kasar nan mu ke bi. Gwamnoni su na da kuri’a daya ne. Ta talakawan da su ke shan wuya a gwamnatin nan mu ke.”
A jiyan ne aka ji cewa shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya taya gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, murnar sauya sheƙa daga jam'iyyar PDP zuwa APC mai mulki.
Asali: Legit.ng