Yanzu-yanzu: Buhari ya zabi hadimarsa matsayin kwamishana a hukumar INEC

Yanzu-yanzu: Buhari ya zabi hadimarsa matsayin kwamishana a hukumar INEC

- Buhari ya gabatar da sunaye hudu gaban majalisar dattawa domin tabbatar da su matsayin kwamishanoni a INEC

- Mutanen hudu idan majalisa ta tabbatar dasu, za su maye gurbin kwamishanonin hukumar da wa'adinsu na gab da karewa

- Ana sauraron wanda shugaba Buhari zai zaba matsayin sabon shugaban INEC

Shugaba Muhammadu Buhari ya zabi hadimarsa ta Soshiyal Midiya, Lauretta Onochie, a matsayin daya daga cikin kwamishanonin hukumar gudanar da zabe ta kasa watau INEC.

Buhari ya gabatar da sunanta da wasu mutane uku gaban majalisar dattawa domin tantancesu da tabbatar da su.

Idan aka tabbatar da ita, Lauretta Onochie, wacce ta shahara da kare Buhari da zagin masu sukarsa a kafafen sada zumunta zata zama daya daga cikin alkalan zabe a Najeriya.

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya karanta wasikar da Buhari ya aike a zauren majalisar.

Sauran da Buhari ya aike da sunayensu sune Prof. Mohammed Sani mai wakiltan jihar Katsina; Prof. Kunle Ajayi mai wakiltan Ekiti, da nd Seidu Ahmed mai wakiltan Jigawa.

KU DUBA: Da duminsa: Sanata Yusha'u Anka ya rigamu gidan gaskiya

DUBA NAN: Bayan watanni 3 da dakatad da shi, gwamnan jihar Bauchi ya mayar da Sarkin Misau kan kujerarsa

Yanzu-yanzu: Buhari ya zabi hadimarsa matsayin kwamishana a hukumar INEC
Lauretta Onochie Hoto: Channels TV
Asali: UGC

A bangare guda, a ranar Litinin, 12 ga watan Oktoba, ‘yan wata kungiyar hadaka ta manyan Arewacin Najeriya ta nuna damuwa game da gum din shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Kungiyar da ke kokarin kawowa cigaba da zaman lafiya a Arewa ta koka da yadda shugaban kasar ya yi tsit, a lokacin da ake kiran ya sake wa hukumomin tsaro zani.

A cewar wannan kungiya COCONEPD, kiran da majalisa su ka yi wa shugaban kasar na daukar mataki, ya isa ya sa gwamnatin tarayya ta yi abin daya dace tun wuri.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu da ke kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada ra'ayi da zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng