Mala Buni ya tsige duka Shugabannin APC, ya damkawa Matawalle Jam’iyya a jihar Zamfara
- Shugaban APC na rikon kwarya ya sauke shugabannin jam’iyya na Zamfara
- Mala Buni ya sallamawa Bello Matawalle rikon jam’iyyar bayan ya dawo APC
- Tsohon Gwamna Abdulaziz Yari ya sallami mukaminsa ga Gwamna na yanzu
Shugaban kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar APC, Mai Mala Buni, ya bada sanarwar ruguza daukacin shugabannin jam’iyya da ke jihar Zamfara.
Jaridar Daily Trust ta ce Mai Mala Buni ya sauke duka shugabannin APC na mazabu, kananan hukumomi da jiha a ranar da aka karbi Bello Matawalle.
Alhai Mai Mala Buni ya bayyana wannan ne yayin da aka yi wa gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle wankan dawo wa jam’iyyar APC daga PDP.
KU KARANTA: 2021: Zabe ya turnuke APC da rikici a Anambra, an ki yi wa Uba mubaya’a
Da yake magana a garin Gusau, babban birnin jihar Zamfara, shugaban rikon kwaryan na APC ya ce gwamna Bello Matawalle ne zai rike jam’iyya a jihar.
Mala Buni ya ce an sauke dukkanin shugabannin jam’iyya da ke rike da mukamai kafin yanzu, ya yi kira a gare su da su ba Matawalle cikakken hadin-kai.
Tsohon gwamna Abdulaziz Yari ya na tare da Buni
Da yake jawabi a wajen taron tarbar gwamna Matawalle, tsohon gwamna Abdulaziz Yari, ya ce ya amince da wannan mataki da jam’iyyarsu ta APC ta dauka.
Yari wanda ya yi mulkin jihar kafin Bello Matawalle ya ba magajin na sa shawarar abin da ya kamata ya yi domin dangatakarsu ta cigaba da tafiya a haka.
KU KARANTA: Ba zan bar PDP ba - Mataimakin Gwamnan Zamfara
Jaridar ta rahoto Alhaji Abdulaziz Yari ya na cewa:
“Za mu ba gwamnan jihar (Bello Matawalle) goyon-baya, ina so in ja hankalinsa ya yi hattara da ‘yan kanzagi, saboda alakar da mu ke da ita, ta daure.”
Zan tafi da kowa a jihar Zamfara - Bello Matawalle
Shi kuwa Mai girma Bello Matawalle ya bayyana cewa zai yi wa kowa adalci a tafiyar jam’iyya.
Rahoton ya ce gwamnonin jihohin Katsina, Borno, Ogun, Plateau, Kano, Kogi , Kaduna, Jigawa, Neja, Kebbi da Kano, da manyan gwamnati sun halarci taron.
A jiyan kun ji cewa Gwamna Matawalle ya yi kira ga masu ruwa da tsaki a jam'iyyar APC a kan su hada kai domin a kawo wa jihar Zamfara cigaba a mulkinsa.
Asali: Legit.ng