Jam’iyyar APC a Jihar Zamfara ta mayar da martani kan shigar Gwamna Matawalle cikin jam’iyyar

Jam’iyyar APC a Jihar Zamfara ta mayar da martani kan shigar Gwamna Matawalle cikin jam’iyyar

  • Ana ci gaba da samun martani kan sauya shekar da Gwaman Bello Matawalle ya yi daga PDP zuwa APC
  • Jam’iyyar APC a Jihar Zamfara ta yi taro domin duba yadda za ta sake fasalin kanta a sabuwar alkiblar
  • Manyan masu ruwa da tsaki a jam’iyyar na kokarin ganin an kare muradun jam’iyyar a cikin jihar

Jam'iyyar APC reshen Jihar Zamfara ta mayar da martani game da sauya shekar da Gwamna Bello Matawalle ya yi daga Jam'iyyar PDP zuwa Jam’iyyar APC.

A wata sanarwa da Sanata Kabiru Marafa ya aike wa kafar labarai ta Legit.ng, jam’iyyar ta bayyana matsayarta game da ficewar gwamnan da matakan da ta dauka kawo yanzu.

Muhimman bukatun masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar APC a Jihar Zamfara

Sanarwar wacce Dokta Mika’ilu Barau ya sanya wa hannu a madadin Sanata Marafa, ta kuma sanar da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar kan matsayin shugabannin jam’iyyar a matakin kasa domin tabbatar da daidaito a tsakanin dukkanin mambobin Jam’iyyar APC a jihar ta Zamfara.

Ga wani sashe daga cikin sanarwar:

“A matsayin wani bangare na sakamakon ababuwan da muka cimma wa a yayin taron, mun bukaci da a jinkirta bukin sauya shekar da aka shirya gudanarwa a Gusau har sai lokacin da kwamitin bangarori uku da suka hada da shugabancin APC a jihar ta Zamfara da na mai sauya shekar da kuma shugabannin Jam’iyyar APC na kasa sai sun hadu sun gana a kan batun sharuddan sauya shekar.
“Sai dai mun fahimci cewa ba za a iya jinkirta bukin ba saboda matakin shirye-shiryen bukin sun kai makura.
“A kan haka, Jam’iyyar APC reshen Jihar Zamfara karkashin jagorancin Mai girma, tsohon Gwamnan Zamfara, Onorabul Abdulaziz Yari, ya yanke shawarar ficewa daga bukin sauya shekar tare da bai wa shugabannin jam’iyyar a matakin kasa damar ci gaba da shirya taron yayin da jam'iyyar ke shirin daukar matakan da suka dace a kai.
“Shugabannin jam’iyyar na kasa sun sanar da reshen jam’iyyar a Jihar ta Zamfara kan kiran musamman da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Onarabul Abdulaziz Yari Abubakar domin ya halarci bukin.
“A kan bukatar da shugaban rikon ya yi ta hannun Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna, shugabannin jihar da na kasa na jam’iyyar sun wakilta Sanata Kabiru Garba Marafa (CON) domin yi wa mambobin bayani game da ci gaban tattaunawa da kuma sharuddan shiga tsakanin da aka yi a Kaduna.

DUBA NAN: Najeriya ce kan gaba a yaran da ba sa zuwa makaranta a yankin Sahara - Ministan Ilimi

Jam’iyyar APC a Jihar Zamfara
Jam’iyyar APC a Jihar Zamfara ta mayar da martani kan shigar Gwamna Matawalle cikin jam’iyyar Hoto: Zamfara State GOVT
Asali: Facebook

DUBA NAN: Ina PDP, ba zan yi butulci ba, ba zan koma APC ba: Mataimakin gwamnan Zamfara

Jiga-jigan jam’iyyar sun gana inda suka ja kunnen gwamnan da ya bi dokokinta sau da kafa

Sanarwar ta nunar da cewa yarjeniyoyin da aka kulla yayin taron na bangarorin uku dukkan bangarorin za su sa ido sosai a kansu.

Ta kara da cewa duk wani yunkurin da gwamnan zai yi na karya sharuddan yarjejeniyar to kuwa za a taka masa birki.

Sanarwar ta bayyana cewa an gudanar da taron ne a otal din Bafra da ke Jihar Kaduna inda Sanata Marafa ya yi zama na musamman tare da mambobin jam’iyyar.

A halin yanzu, duk da sauya shekar da Matawalle ya yi zuwa APC, mataimakin gwamnan jihar, Muhammad Gusau, ya bayyana kudurinsa na ci gaba da kasancewa a Jam’iyyar PDP.

Mataimakin gwamnan ya ki bin Matawalle

Mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Muhammad Gusau, ya lashi takobin cewa zai cigaba da zama a jam'iyyar People’s Democratic Party PDP, duk da cewa gwamnan jihar, Bello Matwalle ya koma All Progressives Congress APC.

Dukkan Sanatocin Zamfara uku, yan majalisar wakilai shida da yan majalisa jiha 24 sun sauya sheka tare da gwamnan illa mataimakinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel