Kungiyar ACTED da Zulum ya dakatar a Borno ta bayyana dalilin da yasa ta ke bawa ma'aikatanta horaswa
- Kungiyar bada agaji na ACTED da gwamnatin jihar Borno ta dakatar ta ce bata saba dokokin Nigeria ba
- Babagana Zulum, gwamnan jihar Borno ya bada umurnin a dakatar da ayyukan kungiyar ne bayan an gano suna koyawa ma'aikatansu harbi
- A bangarenta, kungiyar ta ce halin rashin tsaro da hatsari da ma'aikatanta ke shiga yasa aka shiryawa horaswar amma ba bindigan ake basu ba
Kungiyar bada agaji mai zaman kanta na Faransa ACTED ta ce ta shiryawa wasu ma'aikatanta horaswa na koyon harbin bindiga ne saboda irin barazanar da suka gamuwa da shi a yayin ayyukansu, The Cable ta ruwaito.
A cikin sanarwar da ta fitar a ranar Lahadi, kungiyar ta ce wasu daga cikin ma'aikatanta sun tsinci kansu a 'yanayi masu hatsari sosai ta yadda ba za a iya bada garantin tsaronsu ba.'
DUBA WANNAN: Fastocin takarar shugaban ƙasa na Gwamna Bala Mohammed sun mamaye birnin Kano
Kungiyar na martani ne kan dakatarwar da Gwamnan Borno Babagana Zulum ya yi mata bayan an gano tana koyar da wasu ma'aikatanta yadda ake harbi a wani otel da ke Maiduguri.
Yan sanda sun fara bincike a kan lamarin yayin da aka rufe otel din da aka gano ana bada horaswan.
Martanin ACTED kan dakatarwar da gwamnatin jihar Borno ta yi mata
A sanarwar da ta bawa The Cable, ACTED ta ce ta bi dukkan dokokin jihar Borno da Nigeria a yayin gudanar da ayyukanta na bada agaji a arewa maso gabas.
Kungiyar ta ce yanayin rashin tsaro da bin tsarin ayyuka ne yasa ya zama dole ta kula da ma'aikatanta, ta tabbatar ba abin da ya same su.
KU KARANTA: An kama garada 3 da suka ɗirka wa matar aure ciki kafin shigar da ita 'Ɗarikar Haƙiƙa' a Katsina
Hakan ya kunshi shirya bada horaswa daga lokaci zuwa lokaci da atisaye kamar wanda aka yi a ranar 26 ga watan Yuni domin shirya su fuskantar duk wani abin da ka iya tasowa.
"Wannan atisayen abu ne da kungiyoyin ajagi a Nigeria da kasashen waje ke yi kuma ACTED ba ta yawo da makamai yayin atisayen ko akasin hakan kamar yadda dokokin ayyukansu suka tanada."
Kungiyar ta ce a shirye ta ke ta cigaba da hadin kai da hukumomin Nigeria don ganin ta cigaba da yi wa al'umma hidima ba kuma tare da wani boye-boye ba.
Asali: Legit.ng