Wata mata tana neman mutumin da ta aura a dandalin taron dalibai tun lokacin suna firamare

Wata mata tana neman mutumin da ta aura a dandalin taron dalibai tun lokacin suna firamare

  • Wata mata mai suna Leina, da ke amfani da @_chef2b_ a Tiwita tana neman mutumin da ta aura a lokacin suna makarantar firamare
  • Matar ’yar Uganda tana sa ran sake haduwa da Albert, yaron da ta aura a matsayin auren wasa
  • Ta ce shekaru da dama sun gabata ba tare da ta iya ganin mijinta na yaranta ba; yanzu abin da ya rage a wajenta shi ne tuna lamarin

Wata mata 'yar kasar Uganda mai suna Leina, da take amfani da sunan @ _chef2b_ a shafukan sada zumunta ta shiga shafukan sada zumuntan domin gano wani mutum mai suna Albert wanda ta aura a farfajiyar taron daliban firamare.

A wadancan sheakarun, Leina ta yi aure na ba’a kuma yayin bikin, Albert din ya kasance mijinta.

DUBA NAN: Ina PDP, ba zan yi butulci ba, ba zan koma APC ba: Mataimakin gwamnan Zamfara

Wata mata tana neman mutumin da ta aura suna yara
Wata mata tana neman mutumin da ta aura a dandalin taron dalibai tun lokacin suna firamare Hoto: My Wedding Uganda
Asali: UGC

DUBA NAN: Ina PDP, ba zan yi butulci ba, ba zan koma APC ba: Mataimakin gwamnan Zamfara

Mun yi 'aure' a aji na biyu na firamare

Sai dai lamarin auren ba’ar, bisa dukkan alamu ya yi mata tsaye a rai musamman a yanzu da babu abin da take so illa shi ne ta sake haduwa da Albert.

Yayin da shekaru suka ja babu wani abu da ya rage a hannun Leina shi ne hoto na muhimmin lokacin da suka daura auren ba’ar wanda da alama ba za ta manta da shi ba.

Tana zumudin inda abokin karatun nata yake a yanzu, kamar yadda ta wallafa.

Ma’aurata ’yan Najeriya sun samu ’yan biyu shekara 21 suna jiran haihuwa

A bangare guda, wadansu ma’aurata a Najeriya suna cike da murna da fara’a bayan sun samu karuwa na farko da ’yan biyu bayan shafe fiye da shekara 20 suna zaman jiran tsammani.

Wata dangin ma’auratan mai suna Faith Elvis Ovie ita ce ta sanar da labarin a shafin Facebook ranar 12 ga watan Yuni.

Ta ce jiran nasu ya haifar musu da samun ’yan biyu kuma mutane da dama sun taya su murnar samun alherin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng