Wadansu fitattun ’yan Najeriya 130 sun gargadi Bankin Duniya, IMF kan baiwa Najeriya bashi

Wadansu fitattun ’yan Najeriya 130 sun gargadi Bankin Duniya, IMF kan baiwa Najeriya bashi

  • Gamayyar ta gargadi manyan kasashen duniya game da ci gaba da bai wa Najeriya rance saboda wasu dalilai
  • Ta kwatanta lamarin Najeriya a zaman wani aikin da ake takaddama a kansa
  • Sun ce ba za a yi amfani da kudi ko kuma kadarorinsu wajen biyan lamunin da ke kan Najeriya ba

An gargadi kasashen duniya game da ci gaba da bai wa gwamnatin Najeriya rance kan hujjar cewa a yanzu Najeriya kasa ce da ake sanya alamar tambaya kan rikon cin gashin kanta.

Gargadin hakan ya fito daga wadansu dattawan kasar da jagorori masu hangen nesa wadanda yawansu ya kai 129, da suka sanya hannu a kan kundin tsarin mulkin tilas wanda aka ayyana ranar 16 ga Disambar 2020 a kan Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 karkashin inuwar hadaddiyar kungiyar 'yan asalin Najeriya (NINAS), rahoton Sun.

Sun gargadi Bankin Duniya da Asusun Bada Lamuni na Duniya (IMF) da Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Afirka da Tarayyar Turai da Amurka da Faransa da China da Birtaniya da su daina bai wa gwamnatin Najeriya rance, suna masu cewa ci gaba da lamuni na 'aikin da ake takaddama' kawai za a yi masa fassara da aikin sakaci.

Fitattun daga cikin shugabannin sun hada da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa na Soja a Najeriya, Kwamanda Ebitu Ukiwe (mai ritaya) da tsohon gwamnan Jihar Filato, Jonah Jang da sanannen masanin tarihin nan kuma mamba a Jamhuriya ta biyu a majalisar dattijai, Farfesa Banji Akintoye da tsohon Shugaba kungiyar Ohanaeze Ndigbo, Cif Nnia Nwodo da Farfesa Yusuf Turaki da wadansu fitattu 124.

KU KARANTA: Wata mata tana neman mutumin da ta aura a dandalin taron dalibai tun lokacin suna firamare

Bankin Duniya, IMF kan baiwa Najeriya bashi
Wadansu fitattun ’yan Najeriya 130 sun gargadi Bankin Duniya, IMF kan baiwa Najeriya bashi
Asali: UGC

DUBA NAN: Ina PDP, ba zan yi butulci ba, ba zan koma APC ba: Mataimakin gwamnan Zamfara

Sanarwar da shugaban kwamitin gudanarwa na gamayyar ta NINAS, Otunba Folashade Olukoya, ya raba wa manema labarai a ranar Lahadi, a madadin Sakatariyar ta NINAS, ta nunar da cewa:

“Labarin da NINAS take samu shi ne gwamnatin Najeriya ta kara karbar wasu rancen.
'Bugu da kari, muna tunatar da kasashen duniya cewa Najeriya fa a yanzu tamkar wata kasa ce da ake takaddama kan aikinta. Hakan na kunshe ne a sanarwar bayan taronmu na ranar 16 ga watan Disamba 2020, lokacin da muka ayyana kundin mulki na ala tilas.
“Sauran ababuwan da muka gudanar a bayan nan kamar yadda aka bayyana a taron manema labarai na 17 ga Maris 2021, da 17 ga watan Afrilu 2021 sun jaddada cewa Najeriya ta kasance aikin da ake takaddama a kai. Idan an san da hakan sannan kuma a daya bangaren aka ci gaba da bai wa kasar rance ko lamunin kudi, to za a iya cewa akwai sakaci a abin.

Sun kara da cewa domin cire duk wata tababa ’Yan Asalin Kasa ba za su biya ko kuma a yi tsammanin za su biya irin wadannan rancen ba ko kuma su bayar da damar amfani da kadarorinsu a matsayin jingina domin warware wa ko biyan wannan lamunin ba.’

Najeriya ta talauce, wajibi ne mu cigaba da karban bashi: Shugaban Majalisa

A bangare guda, Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya yi bayanin dalilin da ya sa ya zama wajibi Najeriya ta cigaba da karban basussukan kudi domin aiwatar da ayyuka.

Lawan ya ce bai tunanin ya kamata gwamnati ta cigaba da tatsan yan Najeriya saboda irin matsin tattalin arzikin da ake fama da shi.

Shugaban majalisar ya bayyana hakan ne ranar Alhamis yayinda yake hira da manema labarai bayan ganawa da shugaba Muhammadu Buhari a fadar Aso Villa, rahoton ChannelsTV.

Asali: Legit.ng

Online view pixel