Hatsari Ya Laƙume Rayukan Yan Najeriya 2,233 a Cikin Watanni 4 Kacal, FRSC

Hatsari Ya Laƙume Rayukan Yan Najeriya 2,233 a Cikin Watanni 4 Kacal, FRSC

  • Hukumar FRSC ta bayyana cewa na samu hatsari a kan hanyoyi da suka kai 4,459 a cikin watanni huɗu kacal
  • Hukumar tace aƙalla mutum 28,826 ne hatsari ya rutsa da su a cikin wannan lokacin, kuma mutum 2,233 suka mutu
  • Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola, yace bai kamata a zargi lalacewar hanya ba

Hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa (FRSC), a ranar Litinin, ta bayyana cewa yan Najeriya 2,233 ne suka rasa rayukansu sanadiyyar hatsarin mota a cikin watanni huɗun farko na shekarar 2021, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Da Ɗuminsa: FG Ta Faɗi Ranar da Zata Kulle Layukan Wayar da Ba'a Haɗasu da NIN Ba

Shugaban hukumar, Boboye Oyeyemi, shine ya bayyana haka a wurin wani taro da aka yiwa take da 'Sauka lafiya: Gina hanya domin samun ingantaccen tuƙi.'

Ya ƙara da cewa an samu wannan adadin rasa rayukan ne daga hatsari 4,459, wanda ya rutsa da mutum 28,826 a faɗin ƙasar nan.

Hatsari Ya Laƙume Rayukan Yan Najeriya 2,233
Hatsari Ya Laƙume Rayukan Yan Najeriya 2,233 a Cikin Wanni 4 Kacal, FRSC Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Yace: "Adadin da muka samu daga farkon wannan shekarar ya nuna cewa mutum 691 ne suka mutu a watan Janairu, 497 a watan Fabrairu, 480 a watan Maris da kuma 565 a watan Afrilu."

"Masu amfani da hanyoyi sun ƙara yawa, kuma wannan shine dalilin da ya kawo hatsari da dama a watan Janairu da Afrilu."

Ba rashin kyau na hanyoyi ne yake kawo hatsari ba

Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola, yace bai kamata a zargi rashin kyau na hanyoyi da jawo yawaitar hatsari ba, kamata yayi a zargi direbobi.

KARANTA ANAN: Wani Tsohon Kwamishina Ya Sha da Ƙyar Yayin da Yan Bindiga Suka Buɗe Wa Motocinsa Wuta

Yace: "Idan kana gudu a kan hanyar da kasan bata da kyau, kuma kaji motarka na girgiɗi amma ka cigaba da zuga gudunka, tambayar da zaka yi wa kanka shin ka cancanci kayi tuƙi kuwa?"

A wani labarin kuma Bayan Matawalle, Jam'iyyar PDP Ta Faɗi Babban Dalilin da Yasa Gwamnoni Ke Ficewa Daga Cikinta

Wani jigon babban jam'iyyar hamayya PDP ya bayyana ainihin dalilin da yasa gwamnoni ke guduwa daga jam'iyyar, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

A cewarsa duk gwamnan da ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC to ba shi da dalilin yin hakan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel