Farashin man fetur ya na tashi bayan Gwamnatin Tarayya ta karya darajar Naira

Farashin man fetur ya na tashi bayan Gwamnatin Tarayya ta karya darajar Naira

  • Rahotanni sun bayyana cewa farashin danyen man fetur ya na tashi a kasuwa
  • Bayan tsadar da mai ke yi a Duniya, CBN ya karya darajar Naira kwanakin baya
  • Wannan ne ya haddasa kashe Biliyoyi domin a hana fetur tashi a gidajen mai

Farashin shigo da man fetur Najeriya ya tashi da sama da 60% tsakanin watan Disamban shekarar 2020 zuwa yanzu, jaridar Punch ta fitar da wannan rahoto.

Farashin man fetur ya na yin sama

A karshen shekarar da ta wuce, ana saida litar man fetur a kan N143, a halin yanzu maganar da ake yi, kudin dakon fetur kawai har ya iso gidajen mai ya kai N231.

Duk da sauyin farashin da ake samu, har gobe ana saida fetur ne tsakanin N162 da N165 a Najeriya.

KU KARANTA: Litar man fetur zai iya kai N200 idan babu tallafin mai

A watan da ya wuce babban bankin Najeriya ya karya darajar Naira, ya bada damar a rika saida kowace Dalar Amurka daya a kan N410.25 a maimakon N379.

Bayan haka, danyen mai ya na ta kara tsada a kasuwar Duniya, a karshen makon da ya wuce, sai da aka saida gangar danyen man da ba a tace ba a kan $76.18.

An dawo da biyan tallafin fetur

Binciken da jaridar ta yi ya nuna cewa gwamnatin tarayya za ta kashe sama da Naira biliyan 500 a cikin watanni biyar na farkon bana a kan biyan tallafin man fetur.

Yayin da litar man fetur bai zarce N165 a gidajen mai ba, ainihin kudin sarin fetur ya na tashi a kan N254.90, hakan ya na nufin ana iya samun tazarar fiye da N90.

KU KARANTA: Karin kudin litar man fetur ya riga ya zama dole a yanzu - MAN

Shugaban kamfanin NNPC
Shugaban kamfanin NNPC, Mele Kolo Kyari Hoto: petrobarometer.thecable.ng
Asali: UGC

A karshe gwamnati ce za ta rika biyan wannan gibi na N92.98 da ake samu a kan kowace lita.

Duk da gwamnatin Muhammadu Buhari ta na ikirarin cire hannunta daga harkar fetur, har yanzu kamfanin NNPC ne yake daukar dawainiyar shigo da mai.

A farkon shekarar 2020, gwamnati ta ce ta janye tallafin fetur, wanda hakan ya jawo farashi ya tashi daga N125 zuwa N145, amma tallafin ya dawo daga baya.

A yadda ake shan litoci kusan miliyan 60 na fetur kullum, an bar gwamnatin Najeriya da kashe kimanin N5.58b domin ta iya tsaida farashin lita a yadda ya ke.

A jiya ne karamin Ministan man fetur, Timipre Sylva ya bayyana cewa yayin da ake tsakiyar neman man fetur, an ci karo da arzikin gas mai ‘dan karen yawa.

Garin neman fetur, an yi tuntube da gas malale a kasa wanda zai iya bunkasa tattalin arzikin kasar nan. Adadin gas din da aka gano ya kai kubic tiriliyan 206.

Asali: Legit.ng

Online view pixel