Alkali zai yi hukuncin karshe a kan shari’ar karbe Naira Biliyan 5 daga hannun Dame Jonathan

Alkali zai yi hukuncin karshe a kan shari’ar karbe Naira Biliyan 5 daga hannun Dame Jonathan

  • Patience Jonathan da Hukumar EFCC za su koma kotu nan da watanni uku
  • An cigaba da sauraron shari’ar Mai dakin tsohon shugaban Najeriyar a Legas
  • Za a fara yanke hukunci kan rokon karbe dukiyar Jonathan a watan Oktoba

Wata kotun tarayya da ke garin Legas ta zabi 7 ga watan Oktoba a matsayin ranar da za ta saurari shari’ar hukumar EFCC da Dame Patience Jonathan.

Channels TV ta ce Alkali mai shari’a Tijjani Ringim ya sa wannan rana ne a jiya, 28 ga watan Yuni, 2021, bayan sauraron lauyoyin duka bangarorin.

Za a koma kotu a farkon Oktoba

Alkalin da ke shari’ar ya daga karar domin ya saurari rokon da EFCC ta gabatar. Mai magana da yawun hukumar, Wilson Uwujaren, ya bayyana haka jiya.

KU KARANTA: Patience Jonathan ta soma yin galaba a kan Hukumar EFCC

Mista Wilson Uwujaren ya ce a ranar 7 ga watan Oktoban ne za a sake koma wa kotu, domin a ji ko hukumar EFCC za ta rike dukiyar Jonathan har abada.

Lauyoyi sun yi magana a gaban kotu

Jaridar Premium Times ta ce da aka koma kotu a ranar Litinin, lauyan da ya tsaya wa EFCC, Barista Rotimi Oyedepo, ya dauko tarihin wannan shari’a.

Oyedepo ya shaida wa Alkali cewa wanda ta fara sauraron shari’ar ta yi ritaya daga aiki, amma kafin nan ta bada dama a karbe dukiyar wanda ake zargi.

Lauyoyin Jonathan; Ifedayo Adedipe da Gboyega Oyewole sun roki kotu ta daga shari’ar, ta ba su lokaci mai tsawo domin su kalubalanci hukuncin da aka yi.

KU KARANTA: Uwargidar Jonathan ta kai Hukumar EFCC kara a kotu

Dame Jonathan
Patience Jonathan Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Mai shari’a Ringim ya ce za a dawo nan da watanni hudu, ya ba lauyoyin da suke kare wanda ake zargi tsawon kwanaki 14 su gabatar da takardarsu a kotun.

Shari’ar EFCC da Mai dakin tsohon shugaban Najeriya

EFCC ta na zargin tsohuwar uwargidar kasar Najeriyar da mallakar wasu Dala miliyan $5.78 da Naira biliyan 2.4 (kusan N5bn) ta hanyoyin da ba su dace ba.

Tun a shekarar 2017 aka fara kai Patience Jonathan gaban Alkali Mojisola Olatoregun. Ana tuhumar ta tare da kamfanin La Wari Furniture and Bathes.

A baya kun ji cewa kafin Alkali Mojisola Olatoregun ta ajiye aiki a 2019, ta zartar da hukunci a soma rike dukiyar mai dakin tsohon shugaban kasar da aka samu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng