Sai dai hakuri: Karin kudin litar man fetur ya riga ya zama dole a Najeriya inji Kungiyar MAN

Sai dai hakuri: Karin kudin litar man fetur ya riga ya zama dole a Najeriya inji Kungiyar MAN

- Shugaban kungiyar MAN ya na ganin babu makawa kan tashin farashin fetur

- Segun Ajayi-Kadir ya ce a yau danyen mai ya kara kudi a kasuwannin Duniya

- Matsalar rashin matatu zai taimaka wajen tsadar fetur a gidajen man Najeriya

Kungiyar MAN ta masu kere-kere a Najeriya, ta na ganin ya wajaba a samu sauyi a farashin fetur.

A ranar Laraba, 26 ga watan Mayu, 2021, jaridar Punch ta rahoto MAN ta na cewa babu makawa, sai an yi karin kudin litar man fetur a kasar nan.

Darekta Janar na kungiyar MAN na kasa, Segun Ajayi-Kadir, ya ce ko za a cire tallafin man fetur, ko ba za a cire ba, ya kamata farashin mai ya canza.

KU KARANTA: Kudin sata: Majalisa ta tasa Malami a gaba, ta jefe shi da laifin cin amana

Segun Ajayi-Kadir yake cewa bai kamata a rike farashin lita ba, ya bukaci hukuma ta kyale farashin ya rika yawo a kasuwa gwargwadon bukata.

Shugaban MAN, Ajayi-Kadir, ya bayyana wannan ne a lokacin da ya zanta da ‘yan jarida, bayan gwamnoni sun bada shawarar kara farashi zuwa N385.

Ya ce: “Ya kamata tashin danyen mai ya yi tasiri a kudin litar man fetur a kasar nan, musamman a lokacin da matatun manmu ba su aiki yadda ya dace.”

“Bayan haka, gwamnati ta na ta faman cigaba da biyan kudin tallafin man fetur.” Inji Ajayi-Kadir.

KU KARANTA: Gwamnati ta buga sabon lissafi, za a koma saida fetur a N212

Sai dai hakuri: Karin kudin litar man fetur ya riga ya zama dole a Najeriya inji Kungiyar MAN
Ministan harkar mai, Timipre sylva
Asali: UGC

“Muna da ‘yan kasuwa da ke kutsa kai a harkar shigo da mai, wanda suke bukatar suyi kasuwanci, su samu riba, la’akari da haka, dole farashi ya karu.”

Amma duk da wannan hasashe da kungiyar ta ke yi, Ajayi-Kadir ya na ganin tsaida farashin lita a kan N385, zai taba tattalin arziki ta mummunar hanya.

Brandspurng ta ce MAN ta na ganin wannan kari zai jawo kudin mota ya kara tsada a Najeriya, sannan za a samu karin tsadar rayuwa, ga karancin kudi a hannu.

Kafin yanzu kun ji cewa kungiyar NLC za ta zauna da Gwamnatin Tarayya game da tsaida farashin man fetur da korar Ma’aikatan gwamnati a Jihar Kaduna

Sai bayan zaman ‘Yan kwadago da Gwamnati za a san matsayar tallafin mai. Idan gwamnati ta janye tallafin da ta saba biya, NNPC za ta kara farashin mai a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel