Najeriya ta gano wasu tulin arzikin gas da ba ta taba sanin da zaman su ba inji Minista

Najeriya ta gano wasu tulin arzikin gas da ba ta taba sanin da zaman su ba inji Minista

  • Ministan man fetur, Timipre Sylva, ya ce Gwamnati ta gano arzikin gas a kasa
  • Timipre Sylva ya ce an ci karo da gas din ne yayin da ake kokarin lalubo fetur
  • Idan aka dage, za a iya samun abin da ya kai 600 tcf na gas a malale cikin kasa

Karamin Ministan harkar man fetur na tarayya, Timipre Sylva, ya ce gwamnatin Najeriya ta gano wani tarin arzikin man gas da kasar nan ta mallaka.

Cif Timipre Sylva ya shaida wa hukumar dillacin labarai na kasa cewa a wajen nemo danyen man fetur a cikin kasa, sai aka bankado wani gas da ake da shi.

Najeriya ta na da baiwar arzikin gas

Kamar yadda Ministan ya bayyana wa The cable a birnin tarayya Abuja ranar Lahadi, adadin gas din da aka gano a karkashin kasa ya kai kubic tiriliyan 206.

KU KARANTA: Za mu koma bakin aiki - Tsageerun Neja-Delta

“Mu na da gas sosai a kasar nan. Mu na da kubic tiriliyan 206 a ajiye.”
“Saboda haka an gano wannan adadi ya na kwance a kasa. An samu kubic tiriliyan 206 yayin da ake nemo danyen man fetur, don haka tuntube aka yi.”
“Mu na neman fetur ne, sai mu ka ci karo da gas, a wannan tsautsayi sai mu ka samu 206 TCF.”
“Dalilin haka, abin da mu ka yi imani da shi, shi ne idan muka dage sosai wajen neman gas haka, za mu iya samun har kubic mita tiriliyan 600 a kwance.”

KU KARANTA: Bangaren ‘Yan ta’addan Boko Haram sun yi wa AlKhuraishi mubaya’a

Chief Timipre sylva
Timipre sylva Hoto: www.dailypost.ng
Asali: UGC

Nan gaba gas zai karbe wurin fetur

Jaridar ta rahoto Ministan tarayyar ya na cewa nan gaba za a rika koma wa gas daga fetur. Timipre Sylva yake cewa amma sai an san muhimmancin gas din.
“Mun fara yin kaura, don haka ne mu ka fara yin batun gas. Mu na ganin gas ne mafita nan gaba.”
“Mun fara ne da gawayi wanda yake a dunkule, daga nan mu ka koma wa man fetur wanda ruwa ne, yanzu kuma mu na harin gas wanda arziki ne na iska.”

A baya kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun hallaka barayi da 'yan bindiga masu yawa, bayan haka sun karbe makamai da dama daga hannun wadannan miyagu.

Da farko ‘Yan bindigar sun yi wa sojojin kasa kwantan-bauna, amma daga bisani sojojin suka ci karfinsu, kamar yadda labarin ya zo mana a ranar Lahadin da ta wuce.

Asali: Legit.ng

Online view pixel