Ribar kafa: Gwamnan Zamfara ya zugo wani babban ‘Dan adawa ya tsallako jirgin APC

Ribar kafa: Gwamnan Zamfara ya zugo wani babban ‘Dan adawa ya tsallako jirgin APC

  • Dr. Sani Shinkafi ya ce ya fice daga Jam’iyyar APGA, ya koma APC a jihar Zamfara
  • Tsohon Sakataren na APGA ya amsa kiran Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle
  • Shinkafi ya yi kira ga mutanensa su bi APC, amma ya ce ba zai yi masu dole ba

Dr. Sani Shinkafi wanda ya yi wa jam’iyyar APGA takarar gwamna a jihar Zamfara a zaben 2019, ya bar jam’iyyar hamayyar, inda ya koma APC mai mulki.

Jaridar Punch ta ce Sani Shinkafi ya tabbatar da sauya-shekarsa ne a ranar Litinin, 28 ga watan Yuni, 2021, a gaban wasu dinbin magoya bayansa a gidansa.

Dr. Shinkafi ya bayyana cewa Mai girma gwamnan Zamfara, Bello Matawalle ne ya yi masa tayin ya koma jam’iyyar APC, shi kuma ya amsa wannan gayyata.

KU KARANTA: Gwamnan Zamfara, Matawalle ya koma Jam'iyyar APC

Kamar yadda mu ka fahimta, wannan ya tabbatar da cewa gwamnan na Zamfara zai koma APC.

Cigaban jiha ta sa ni sauya-sheka ba kwadayi ba

Channels TV ta rahoto tsohon ‘dan takarar gwamnan ya na cewa ba kwadayin abin Duniya ta sa ya yi watsi da APGA ba, ya ce ya amsa kiran kawo gyara ne.

“Masu tunanin cewa na je jam’iyyar APC ne saboda neman abin Duniya, sun yi kuskure.”
“Zan bar jam’iyyar APGA ba domin ba na son ta ba, ina barin jam’iyyar ne domin amsa tayin da Bello Matawalle ya yi mani a APC na gyara jihar Zamfara.”
“Mai girma Gwamna Bello Matawalle da kansa ya gayyace ni in bi shi zuwa jam’iyyar APC, saboda haka, ban ga dalilin da zai hana ni amsa kiransa ba.”

KU KARANTA: Kusoshin Jam’iyya su na hangen kujerar Shugaban APC na kasa

Dr. Sani Shinkafi
Sani Shinkafi ya na bada sanarwar komawa APC Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Jam’iyyar APGA ta yi babban rashi

Shinkafi ya ce da su aka kafa APGA, kuma ya shafe shekaru 19 a jam’iyyar har ya zama mata sakatare na kasa, kafin yanzu guguwar APC a dauke shi.

“Ba zan matsa wa kowa ya shiga APC ba, kuma zan cigaba da alaka da wadanda su ka zauna a APGA saboda tsohuwar dangantakar da ke tsakaninmu.”

A farkon makon nan ne rahoto ya zo mana cewa Jam'iyyar PDP ta fusata bayan ta ji cewa gwamnan jihar Zamfara ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC.

Hakan ya sa jam'iyyar PDP ta garzaya kotu domin ta kalubalanci wannan mataki da gwamnan ya dauka na barin jam'iyyar da ta yi masa riga da wando a zaben 2019.

Asali: Legit.ng

Online view pixel