Gwamnonin Jihohi sun yi damara, bangaren Buhari sun ci burin karbe shugabancin APC
- Daga watan gobe za a soma gudanar da zaben Shugabanni na Jam’iyyar APC
- Jiga-jigan Jam’iyya su na lissafin yadda za su karbe kujeru a zaben da za a yi
- Bangaren CPC su na kwadayin ganin sun tashi da mukamin shugaban APC
Kwanaki kadan da kara wa kwamitin Mai Mala Buni wa’adi, jiga-jigan APC mai mulki sun fara lissafin yadda za su karbe shugabancin jam’iyya.
Lissafin 2023 ya kankama
Jaridar Punch ta fitar da rahoto cewa manyan jam’iyyar APC, musamman gwamnoni da masu harin zama shugaban kasa a 2023 sun fara yin aiki.
Wadannan jiga-jigan jam’iyya suna kokarin ganin yadda na-kusa da su za su samu shugabanci a matakai dabam-dabam, domin a iya cin nasarar zabe.
KU KARANTA: Gwamnan Zamfara ya canza lissafin 2023, ya bar PDP
Akwai manyan bangarori hudu da suka hadu suka kafa jam’iyyar APC, sune tsofaffin jam’iyyun adawa na CPC, ANPP, ACN da bangaren ‘yan tawaye a PDP.
Wannan tsari aka bi wajen dauko shugabannin jam’iyyar da aka yi a baya Bisi Akande ya fito daga ACN, sai aka dauko John Odigie-Oyegun daga sashen APP.
Bayan nan sai Adams Oshiomhole ya karbi rikon jam’iyyar, shi ma ya fito ne daga bangaren ACN. Daga nan ne sai Mai Mala Buni ya karbi rikon–kwarya.
Gwamna Mai Mala Buni yana cikin wadanda su ke karkashin jam’iyyar ANPP a baya. Hakan ya sa bangaren CPC suke ganin ya kamata su samu kujerar.
KU KARANTA: Ba a tunanin karawa ‘yan kasa haraji - Mataimakin shugaban kasa
Bangaren CPC suna so su kawo shugaban jam’iyya
Shugaba Muhammadu Buhari ya fito ne daga bangaren CPC. Asalin na kut-da-kut da shugaban kasar su na ganin lokaci ya yi da za su samu kujerar.
Rahoton ya ce cikin wadanda su ke wannan tafiya akwai gwamnonin jihohi masu ci, Ministocin tarayya da manya-manyan hadiman shugaban Najeriya.
Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule shi ne kan gaba wajen wannan kamfe, inda yake mara wa tsohon gwamnan Nasarawa, Sanata Tanko Al-Almakura.
Shi ma Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya na da mutanensa da za su nemi a gwabza wajen neman shugabancin jam’iyyar, a ciki akwai wasu ‘yan majalisa.
A makon jiya Uwar jam'iyyar APC ta tsawaita wa'adin kwamitin shugabannin rikon kwaryar dake karkashin jagorancin Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni.
Asali: Legit.ng