Gwamnatin Buhari za ta rika tatsar kudin-shiga a hannun irinsu Facebook da Twitter

Gwamnatin Buhari za ta rika tatsar kudin-shiga a hannun irinsu Facebook da Twitter

  • Farfesa Yemi Osinbajo ya ce za a daura haraji a kan manyan kamfanonin sadarwa
  • Mataimakin shugaban kasar yake cewa kamfanonin suna samun kudi a kasar nan
  • Osinbajo ya tabbatar da cewa babu shirin kara wa mutane haraji cikin shekarar nan

Za a yi amfani da sababbin dokoki wajen karban haraji daga cikin ribar da kamfanonin fasaha da dandalin zamanin gida da waje da suke aiki a Najeriya.

Mai girma mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ya bayyana wannan yayin da ya hadu da tawagar kungiyar CITN ta masu ilmin karbar haraji na kasa.

Shugaban wannan kungiya, Adesina Adedayo, ya jagoranci mutanensa zuwa fadar shugaban kasa a Abuja domin su hadu da mataimakin shugaban kasar.

KU KARANTA: Ana shirin hana shigo da tulun gas a Najeriya

Vanguard ta ce tawagar ta kunshi; Samuel Olushola Agbeluyi, Dame Simplice, James Naiyeju, Muhammad Mainoma, Babangida Ibrahim da Adefisayo Awogbade.

PM News ta ce mai magana da yawun mataimakin shugaban kasa, Laolu Akande ya bayyana wannan.
“Yayin da gwamnatin tarayya ba za ta kara haraji a wannan lokaci ba, saboda dokar tattalin arziki ta bada damar a fadada wuraren da ake samun kudin-shiga”
“Daga cikin inda za a karada har da karbar haraji a hannun manyan kamfanonin fasaha na Duniya da suke samun kudi a Najeriya, da suke cin moriyar zamansu.”

KU KARANTA: Buhari ya ja kunnen masu shirin fasa bututun mai

Gwamnatin Buhari za ta rika tatsar kudin-shiga a hannun irinsu Facebook da Twitter
Farfesa Yemi Osinbajo Hoto: www.bbc.com
Asali: UGC

“Ko da kuwa ba za su kafa wani ginin ofis ba, muddin dai ba su biyan wani haraji a Najeriya.”

Sashe na hudu na dokar tattalin arziki ta shekarar 2019 ya ba Ministan tattalin arziki ikon kayyade abin da ake nufi da kamfanoni su na cin moriyar zama a kasar.

Hadimin mataimakin shugaban Najeriyar ya ce an shiga matsin lambar tattalin arziki, wanda hakan ya yi sanadiyyar da dole ba za a iya karbar harajin yadda aka so ba.

Ana so Alkali ya haramta wa shugaban Najeriya zuwa asibitocin kasar waje da kuma daukar jiragen fadar Shugaban kasa da ake yi zuwa ketare yayin da yake jinya.

Kamar yadda mu ka ji labari, wani lauya ya bukaci Kotu ta hana Gwamnati kashe kudi wajen kai Shugaban kasa asibitin kasar waje domin hakan ya saba wa dokar kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel