Jami'an Sojoji sun hallaka ‘yan bindiga da dama a Zamfara
- Sojoji sun hallaka barayin daji masu yawa tare da kwace makamai da dama
- ‘Yan bindigar sun yi wa dakarun sojin kwantom bauna amma daga bisani sojojin suka ci karfinsu
- Babban Hafsan Sojojin Kasa ya bukaci dakarun sojin da su ci gaba da himmar yaki da barayin dajin
Helkwatar rundunar sojin kasa na Najeriya ta ce sojojin da ke yaki da aika-aikar barayin daji sun kashe barayin dajin masu yawan gaske wadanda ke ta’asa a kauyukan Mayanchi-Dogo Karfe da Fagantama da ke Karamar Hukumar Talata Marafa a Jihar Zamfara.
Daraktan hulda da jama’a na rundunar sojin kasa Birgediya Janal Onyema Nwachukwu, wanda ya sanar da hakan ya ce a yayin da sojojin da ke aiki a karkashin runduna ta takwas suke sintiri sun fuskanci harin kwantom bauna daga barayin dajin inda nan take suka mayar da martani tare da kashe barayin dajin da dama.
Ya ce:
“Dakarun sojin da ke aiki a runduna ta 8 a yayin da suke sintiri sun fuskanci harin kwanton bauna daga barayin dajin da suka addabi kauyukan Mayanchi-Dogo Karfe da Fagantama da ke cikin Karamar Hukumar Talata Marafa a Jihar Zamfara.
“A yayin barin wutar da ya kaure tsakaninsu, sojojin sun yi galaba a kan barayin dajin ta hanyar amfani da manyan makaman da suka fi na barayin.
“Hakan ya haddasa mutuwar barayin dajin da daman gaske. Sojojin sun kuma kwato bindigar PKT guda daya da kunshin albarussai da ma babur guda
A wani lamarin mai nasaba da wannan, dakarun sojin sun kuma yi nasarar hallaka barayin daji guda biyar a wani kauyen da ake kira Bingi a Karamar Hukumar Bungudu cikin Jihar Zamfara,Janal Onyeama ya kara
Yace yayin musayar wutar barayin dajin sun tsere bayan da suka ji mununanan raunukan harbin bindigogi.
A cewarsa:
“Dakarunmu sun kwato bindigar AK47 guda da babur daya da wayoyin hannu guda uku daga wadannan barayin dajin.
“Yayin da muke jinjina wa jarumtar yakin da dakarun suke nuna wa, Babban Hafsan Sojan Kasa na Najeriya Manjo Janal Faruk Yahaya ya bukaci dakarun da su ci gaba da nuna jarumtar fadan da zimmar yakar dukkanin ‘yan ta’addan da suka addabi jihohin Arewa maso Yamma da ma daura sassan kasar nan.”
Sannan ya bukaci al’ummomin jihohin Arewa maso Yamma da su taimaka wa sojojin da bayanai masu muhimmanci a kowane lokaci domin karfafa yaki da ‘yan bindigar.
Asali: Legit.ng