Yawan sauya-sheka da ake yi zuwa APC ya sa an huro wuta a tunbuke Shugaban PDP

Yawan sauya-sheka da ake yi zuwa APC ya sa an huro wuta a tunbuke Shugaban PDP

  • Kungiyar wasu matasan PDP sun koka a kan yadda ake tafiyar da Jam’iyya
  • South-South Youth Vanguard ya na so a kori Shugaban PDP, Uche Secondus
  • Kassim Afegbua da aka kora daga PDP ya na cikin masu mara wa SSYV baya

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa wasu matasa a jam’iyyar PDP sun fara kiran ayi maza-maza a sauke shugaban jam’iyya na kasa, Prince Uche Secondus.

Matasan jam’iyyar na yankin Kudu a karkashin tafiyar South-South Youth Vanguard, suka fitar da jawabi, su na Allah-wadai da asarar da jam’iyyar ta ke ta yi.

Shugaban South-South Youth Vanguard, James Efe Akpofure, ya yi kira ga shugabannin jam’iyyar hamayyar su kawo karshen ficewa daga PDP da manya su ke yi.

KU KARANTA: Sanatan PDP ya sauya sheka zuwa APC, ya hadu da Buhari

Mista James Efe Akpofure wanda ya fito daga yanki daya da Uche Secondus ya na ganin akwai babbar matsala a gaban PDP idan har aka cigaba da tafiya a haka.

Jaridar The Independent ta rahoto Efe Akpofure ya na cewa muddin ba a dauki matakin gyara ba, kafin Uche Secondus ya bar ofis, babu wanda zai rage a cikin PDP.

Kassim Afegbua ya na tare da South-South Youth Vanguard

Kassim Afegbua wanda aka kora daga PDP ya na cikin masu goya wa South-South Youth Vanguard wajen wannan kira, inda ya fitar da jawabi a ranar Lahadi.

Kassim Afegbua yake cewa girman kai ya jawo ana rasa ‘ya ‘yan jam’iyya, ga zabe na zuwa.

Shugaban PDP na kasa
Mr. Prince Uche Secondus Hoto: www.allnigeriainfo.ng
Asali: UGC

KU KARANTA: Matawalle ya sa ranar barin PDP, ya shiga APC

“Lokacin da na fara kai kukan cewa ana rasa ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP a karkashin jagorancin Mista Uche Secondus, an dauka cewa kurum ihu nake yi a banza.”
“Abin da ya faru a wata dayan nan, na sauya-shekar manya PDP zuwa APC ya sake nuna majalisar Uche Secondus ba ta da kan gado, abin a dauki mataki ne.”

PDP ta rasa manyan kujeru a ‘yan watanni

Wadannan matasa sun fara wannan kira ne bayan ganin yadda jam’iyyar hamayyar ta ke rasa kujeru zuwa APC a ‘yan kwanakin bayan nan da suka wuce.

Kungiyar matasan ta na ganin akwai gazawar Prince Uche Secondus ganin yadda PDP ta rasa gwamnan jihar Kuros-Riba, Ben Ayade zuwa jam’iyyar APC.

Ana cikin haka ne kuma sai aka ji cewa Sanata Peter Nwaoboshi ya sauya-sheka bayan dakatar da shi.

Har ila yau ku na da masaniya cewa fadar shugaban ƙasar Najeriya ta tabbatar da sauya sheƙar gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, daga PDP zuwa APC a jiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel