Majalisa ta na neman Amaechi ya zo ya yi bayanin Naira Biliyan 160 da aka ki dawo da su

Majalisa ta na neman Amaechi ya zo ya yi bayanin Naira Biliyan 160 da aka ki dawo da su

  • Majalisar Wakilan Tarayya ta na binciken aikin da NPA ta yi a shekarar 2016
  • Shugabannin hukumar da Minista za su je Majalisa su gabatar da karin bayani
  • Za a ji inda hukumar NPA ta kai Naira Biliyan 166 shekaru biyar da suka wuce

A ranar Alhamis, 24 ga watan Yuni, 2021, Punch ta fitar da rahoto cewa ana binciken wasu biliyoyin kudi da NPA ta ki dawo da su cikin asusun gwamnati.

Jaridar ta ce majalisar wakilan tarayya ta gayyaci Ministan sufuri, Rotimi Amaechi da shugabannin NPA su zo, su yi karin-haske kan Naira biliyan 166.69.

Kwamitin majalisa da ke binciken kudin al’umma ya bayyana cewa hukumar ba ta yi bayanin wannan kudi a takardun da ta gabatar a karshen shekarar 2016 ba.

KU KARANTA: ‘Yan Majalisa sun gano NPA ta karkatar da Dalolin kudi zuwa asusun NSA

The Guardian ta ce an aika wa babban Ministan sufurn sammaci ya bayyana a gaban kwamitin Hon. Wole Oke, a ranar 8 ga watan Yuli, 2021, domin a ji ta bakinsa.

Binciken da ‘Yan majalisa suke yi

Da yake magana a ranar Alhamis, Wole Oke, ya ce sun dauki wannan mataki ne bayan shugabannin NPA da NRC sun ki amsa takardun da aka aika masu.

Oke ya ce:
“Muna sa rai su ba mu amsa a kan binciken kudin da mu ke yi, daga wasu kalamai da babban mai binciken kudi na kasa ya yi a game da abin da NPA ta kashe a 2016.”
“Ana sa ran su gabatar da bayani dalla-dalla na duk abin da NPA ta samu daga kudin shiga, harajin da ake biya a kai-a kai, da kudin haya da suka bada, da sauransu.”
Ministan sufuri
Rotimi Amaechi Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

KU KARANTA: Buhari ya fitar da sabon mukami, ya nada shugaban hukumar NSC

Zargin da ke kan Ministan sufuri da NPA

“Babban mai binciken kudi ya ce Ministan da shugabannin NPA za su amsa tambayoyin ‘yan majalisa kan abin da aka batar wajen gyaran hanyoyin da na’urori.”

Wadanda ake zargi za su yi bayanin inda suka kai N643.006m da aka samu daga abokan hulda. Sannan ana zargin NPA ta yi facakar kashe Naira biliyan 61 a shekarar.

Har ila yau binciken da gwamnatin tarayya ta yi, ya nuna an biya kamfanin Intels a matsayin kamasho, wanda wannan ya zarce abin da ya kamata kamfanin ya samu.

A jiya kun ji cewa rashin fitowa yi wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari maraba yayin da ya ziyarci garin Maiduguri ta ja an sallami wani ‘dan makaranta a jihar Borno.

Mun ji cewa asali ma har yara 20 aka dakatar daga makaranta saboda sun ki fitowa tarbar Buhari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel