Albashin Ma’aikata: Gwamnatin Buhari ta shirya yin wasu ‘yan kwaskwarima inji OHCS

Albashin Ma’aikata: Gwamnatin Buhari ta shirya yin wasu ‘yan kwaskwarima inji OHCS

  • Gwamnatin Tarayya ta dage a kan gyara tsarin albashin Ma’aikatan kasar
  • Folasade Yemi-Esan ta ce maganar ta yi nisa, an kafa kwamiti ya na aiki
  • Shugaban ma’aikatan kasar ta ce an biya magada kusan 600 hakkokinsu

Gwamnatin tarayya ta sake jaddada cewa ta shirya daidaita kan albashin da ma’aikatanta suke karba. Jaridar Daily Trust ta fitar da wannan rahoton a jiya.

Shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya, Dr. Folasade Yemi-Esan, ta ce da gaske su ke yi wajen ganin an yi gyara a kan abin da ake biyan ma’aikatan gwamnati.

Dr. Folasade Yemi-Esan ta yi wannan magana ne a ranar Alhamis, 25 ga watan Yuni, 2021, a wajen wani taron da manema labarai suka shirya a makon nan.

KU KARANTA: Mun taimaki rayuwar mutum miliyan 11 - Minista

Ana wannan zama ne domin ayi bikin tuna wa da ma’aikatan gwamnati. Makasudin zaman bana shi ne yadda za a iya gyara aikin gwamnati a kasashen Afrika.

Kamar yadda jaridar ta bada rahoto, Folasade Yemi-Esan ta ce an kai ga kafa wasu kananan kwamitoci da za su yi wannan aiki, domin ba lamarin muhimmanci.

An dade ana kiran a yi garambawul wajen tsarin albashin ma’aikata. Ana ganin yin hakan ne zai jawo a kawo karshen koke-koken rashin adalci da wasu su ke yi.

Jawabin Dr. Folasade Yemi-Esan

“Mun yi taro biyu, bayan nan muka bada wata guda domin a gabatar da rahoto ga babban kwamiti.”

KU KARANTA: Majalisa na neman Minista a kan zargin facaka da N166b a NPA

HCS a Aso Villa
Dr. Folasade Yemi-Esan Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC
“Saboda haka da zarar an kammala aikin, ko da yake abin akwai hadari, ina mai iya sanar da ku cewa kwamitin da aka kafa zai dauki mataki, ya yi abin da ya dace.”
“Har yanzu ana tsakiyar aikin ne, za su samu rahoton da zarar mun karkare komai da komai.”

Hakkokin ma’aikatan da su ka rasu

Bayan haka, shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayyar ta ce an ware Naira biliyan N2.468 wajen biyan hakkokan mutane 594 da suka mutu, su na aiki a Najeriya.

A iya da yamma aka ji cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fitar da sabon mukami, ya ba Emmanuel Jime kujerar hukumar NSC, ana shirin zai bar kasar.

Emmanuel Lyambee Jime ne sabon Shugaban hukumar kula da kayan fatauci na kasa. Tsohon 'dan majalisar zai yi shekaru hudu ya na rike da wannan kujera.

Asali: Legit.ng

Online view pixel