Ofishin kula da kasafin kudi ya goyi bayan Ahmed Lawan, ta ce Najeriya ta talauce

Ofishin kula da kasafin kudi ya goyi bayan Ahmed Lawan, ta ce Najeriya ta talauce

  • Babban Daraktan Ofishin Kula da Kasafin Kudi ya ce dole ne Najeriya take cin bashi
  • Sannan ya ce lallai ne ’yan Najeriya su yarda cewa kasar mataulaciyar kasa ce
  • Ya nunar da cewa babu kasar da ba ta karban bashi a duniya

Ofishin kula da kasafin kudi na tarayya ya ce dole ne ’yan Najeriya su yarda cewa kasarsu matalauciyar kasa ce sai dai za ta iya zama attajirar kasa a gaba.

Ofishin ya kuma ce lallai ne fa kasar ta ci gaba da karbo rancen kudi domin fitar da kanta daga kangin komadar tattalin arzikin da take fama da shi.

Babban Daraktan ofishin, Ben Akabueze, ya sanar da hakan ne a zaman martani bayan kalaman da Shugaban Majalisar Dattijai, Ahmad Lawan, ya yi kan karbo bashin da kasar ke yi yayin da yake ganawa da ’yan jarida a ranar Alhamis a fadar Shugaban Kasa bayan ya gana da Shugaba Muhammadu Buhari.

KU KARANTA: Yan sanda sun arce yayin da sojoji suka kutsa caji ofis a Osun

Ofishin kula da kasafin kudi ya goyi bayan Ahmed Lawan
Ofishin kula da kasafin kudi ya goyi bayan Ahmed Lawan, ta ce Najeriya ta talauce Hoto
Asali: UGC

DUBA NAN: An rufe yin rijistan Hajjin Bana a Saudiyya, mutum 540,000 suka yi rijista, za'a zabi 60,000

Mista Akabueze, ta cikin shirin ‘Politics Today’ da kafar telebijin din Channels ranar Alhamis da daddare ya soki wadanda ke sukar tarin bashin da ke kan kasar.

Yace:

“Da farko yana da muhimmanci ’yan Najeriya su fahimci cewa kasarmu ba mai arziki ba ce ita; za mu dai iya zama kasa mai arziki nan gaba.
‘’Amma zancen gaskiya a yanzu dai kasarmu mataulaciya ce saboda lura da ma’anar talauci cewa a duk lokacin da abin da ke hannunka ba ya iya biya maka bukatunka, to kai talaka ne.
‘’A matakin daidakun mutane, za a ce lamarin ya sha bamban saboda abin da za ka yi yana da sauki. Amma idan ana batun kasa guda, abin akwai sarkakiya.

Ya kara da akwai wadansu muhimman nauyeyen da suka rataya a wuyan gwamnatin da za ta sauke wa jama’ar kasa. Sannan a ko ina a duniya, karbo rance na daga cikin ababuwan da gwamnatoci suke yi muddin dai suna da kudurin dorewar lamuran kasar.

Mu daina yaudarar kanmu, mun talauce - Ahmad Lawan

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya yi bayanin dalilin da ya sa ya zama wajibi Najeriya ta cigaba da karban basussukan kudi domin aiwatar da ayyuka.

Lawan ya ce bai tunanin ya kamata gwamnati ta cigaba da tatsan yan Najeriya saboda irin matsin tattalin arzikin da ake fama da shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel