Gwamnatin Tarayya ta ba tsohon ‘Dan wasan Chelsea, Mikel Obi mukami a Najeriya

Gwamnatin Tarayya ta ba tsohon ‘Dan wasan Chelsea, Mikel Obi mukami a Najeriya

  • Gwamnatin Najeriya ta zabi John Mikel Obi a matsayin Jakadan matasa
  • Sunday Dare ya bada wannan sanarwa a filin wasan Legas yau da rana
  • 'Dan kwallon na kungiyar Stoke City ya ji dadin mukamin da aka ba shi

Gwamnatin tarayya ta nada tsohon mai rike da kambun ‘yan wasan kwallon kafan Najeriya, John Mikel Obi, a matsayin Jakadan matasa na kasar nan.

Punch ta fitar da rahoto a ranar Juma’a, 18 ga watan Yuni, 2021, cewa an ba John Mikel Obi wanan kujera ne domin ya zaburar da matasan da ke Najeriya.

Ministan wasanni da harkokin matasan tarayya, Mista Sunday Dare, ya bada wannan sanarwa a wani biki da aka shirya a filin wasa na Surulere, jihar Legas.

KU KARANTA: Sergio Ramos ya yi sallama da Real Madrid

Mikel Obi ya cancanci wannan matsayi

Mai taimakawa Mai girma Ministan wajen harkokin yada labarai, John Joshua-Akanji, ya fitar da jawabi, ya na bayanin abin da ya sa aka zabi John Mikel Obi.

Ministan ta bakin hadimin na sa Joshua-Akanji, ya bayyana tauraron ‘dan wasan a matsayin ‘abin koyi’ wanda ya bar tarihi a harkar cigaban wasan kwallo.

Har ila yau, Ministan ya ce tsohon ‘dan wasan tsakiyan yana canza rayuwar matasa a kasar nan.

Gidan talabijin na Channels TV ta rahoto Sunday Dare ya na cewa gwamnatin tarayya a shirye ta ke ta taimaka wa Obi a duk lokacin zai ba kasarsa gudumuwa.

KU KARANTA: Ronaldo ya jawowa kamfanin lemun Coca Cola asara

Minista tare da Mikel Obi
Sunday Dare da Mikel Obi Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Jawabin Ministan wasanni, Sunday Dare

“Lokaci ba zai ba ni damar magana a kan nasarorin da Mikel ya samu a kwallon kafa ba. Gwaninmu ne kuma abin koyi da ya yi tasiri a rayuwar matasa.”
“Abin alfahari na ne in nada ka a matsayin Jakadan matasa. Wannan sabuwar kujera ce, za a sanar da ‘yan Najeriya a kan wannan mukami da aka ba ka.”

Shi kuwa Obi ya ce:

“An karrama ni da aka zabe ni a matsayin Jakadan matasan kasar nan, na yi farin ciki, zan yi bakin kokari na domin ba matasanmu kwarin-gwiwa."

Asali: Legit.ng

Online view pixel