An wanke tsohon Gwamna da alaka da Boko Haram yayin da yake neman kujerar Shugaban APC

An wanke tsohon Gwamna da alaka da Boko Haram yayin da yake neman kujerar Shugaban APC

  • Kassim Kassim ya na goyon bayan Ali Modu Sheriff ya zama sabon Shugaban APC
  • Hon. Kassim ya ce karya ne a ce Modu Sheriff ya na da hannu a rikicin Boko Haram
  • Tsohon ‘Dan Majalisar ya na ganin tsohon Gwamnan ya cancanci ya rike Jam’iyya

Wani tsohon ‘dan majalisa a jihar Nasarawa, Kassim Kassim, ya ce zargin da ake yawan yi wa Ali Modu Sheriff na alaka da Boko Haram, rashin adalci ne.

Jaridar Premium Times ta ce Honarabul Kassim Kassim ya wanke tsohon gwamnan na jihar Borno, ya ce kazafi ake yi masa, wanda hakan bai dace ba.

Kazafi ake yi wa Ali Modu Sheriff

Kassim ya na maida martani ne ga masu zargin Sanata Modu Sheriff da cewa shi ne kashin-bayan ‘yan ta’addan Boko Haram, wanda ya rika ba su dukiya.

KU KARANTA: Sanata Ali Modu Sherrif ya gana da Buhari bayan zaben 2019

Tsohon ‘dan majalisar dokokin ya ce Ali Modu Sheriff wanda yanzu yake sha’awar zama shugaban APC na kasa, ya musanya wannan zargin tun tuni.

A cewar Kassim Kassim, da a ce da gaske tsohon gwamnan na Borno ya na da dagantaka da ‘yan ta’adda, da tuni jami’an tsaro sun kama shi, an hukunta shi.

Har ila yau jaridar ta rahoto Kassim ya na cewa idan da zargin gaskiya ne, da gwamnatin jihar Borno ko gwamnatin tarayya sun fallasa laifin Sanata Sheriff.

Ya ce:

“Tun ranar 10 ga watan Disamban 2014, DSS su ka wanke shi daga zargi. A rahotonta, DSS ta ce Stephen Davis da wasu sun hadu domin su bata sunan Sheriff, da tsohon shugaban APC na Borno, Mala Othman, a matsayin masu taimaka wa Boko Haram.”
Manyan APC
Ali Modu Sheriff da manyan APC Hoto: www.icirnigeria.org
Asali: UGC

KU KARANTA: Buhari ya yi zama da Gwamnonin jihohin Arewa a fadarsa

Takarar kujerar Shugaban APC na kasa

Hon. Kassim ya na ganin Modu Sheriff ya cancanci ya rike APC ganin shi ne gwamnan da ya fara tazarce a Borno, kuma ya yi shekaru takwas a majalisar dattawa.

‘Dan siyasar ya ce Sanata Sheriff ne ya dauko Kashim Shettima, ya yi kokarin da ya yi wajen ganin ya zama gwamna, a wancan lokacin Shettima ya na banki.

“A 1992, Sheriff ne ya doke mai dakin Babagana Kingibe ya zama Sanatan Borno, ya sake lashe wannan kujera a lokacin Janar Sani Abacha da zaben 1999.”

Dazu kun ji cewa akwai wasu Gwamnonin jihohin da ba su kai ga kammala wa’adinsu ba, amma Magoya baya su na zuga su a kan su fito neman takarar shugaban kasa.

Yahaya Bello, Aminu Tambuwal suna cikin Gwamnonin da ake tunanin su na harin zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel