Ali Modu Sherrif ya gana da Buhari, ya fadi dalilin da yasa mutan Borno suka zabe shi

Ali Modu Sherrif ya gana da Buhari, ya fadi dalilin da yasa mutan Borno suka zabe shi

Baya ga cece-kuce da aka rika yi bisa adadin kuri'un da aka samu daga jihar Borno a zaben shugaban kasa da 'yan majalisun tarayya da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairun 2019, Tsohon gwamnan Borno Ali Modu Sheriff ya bayyana cewa dirkake kungiyar Boko Haram da wasu nasarori da gwamnatin Shugaba Buhari ta samu yana daga cikin dalilan da ya sanya al'umma da yawa suka fito suka yi zabe a jihar.

Idan ba a manta ba dai a zaben na ranar Asabar da ta gabata, shugaba Muhammadu Buhari na APC ya samu kuri'u 836,496 inda ya doke babban abokin hammayarsa Atiku Abubakar na PDP da ya samu kuri'u 71,788 a jihar.

Ali Modu Sherrif ya gana da Buhari, ya fadi dalilin da yasa mutan Borno suka zabe shi
Ali Modu Sherrif ya gana da Buhari, ya fadi dalilin da yasa mutan Borno suka zabe shi
Asali: Facebook

A yayin da ya ke magana da manema labarai a ranar Juma'a bayan ganawar sirri da Shugaba Buhari a fadar Aso Villa, Mr Modu Sherrif ya bayyana cewa ya yi tsamanin za a samu kuri'u fiye da abinda aka samu a jihar.

DUBA WANNAN: Taron sulhu: Atiku ya gabatarwa Buhari wasu muhimman bukatu 5

A cewarsa, hare-haren da 'yan ta'adda suke kaiwa a wasu sassan jihar ne ya sanya al'ummar jihar ba su baiwa Buhari kuri'u kasa da Miliyan Biyu ba a zaben da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata.

"Ban san abinda ya sa PDP ke guna-guni ba a garin da muke da masu rajistan zabe fiye da Miliyan Biyu kuma kawai kuri'u 830,000.

"A lokacin da na ke na gwamna, shugaban kasa ya samu kuri'u fiye da miliyan daya a Borno; Mene yasa ba suyi korafi a wannan lokacin ba? Kawai suna kwakwazo ne," inji Sherrif.

Tsohon gwamnan ya kara da cewa bai taba ganin zabe mai inganci irin wannan ba a Najeriya, ya kuma ce Shugaba Muhammadu Buhari aiki ya sa a gaba ba wawure dukiyar al'umma ba hakan ya sa al'umma ke kaunarsa sa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel