Tallafin rayuwa: Mun kashe wa ’yan Najeriya miliyan 11 Dala miliyan 415 – Minista

Tallafin rayuwa: Mun kashe wa ’yan Najeriya miliyan 11 Dala miliyan 415 – Minista

  • Ministar ta ce shirin ya gudanar da ayyukan tallafin a kananan hukumoni 543 cikin jihohi 29 da Abuja da ke cikin shirin
  • Ta ce an faro shirin ne tun a shekarar 2009 har zuwa yanzu yake gudana
  • Ta bayyana dabarun da ake bi wajen gano talakawa da gajiyayyun cikin jama’a

Ministar Jin Kai da Kula da Bala’o’i, Sadiya Umar Farouq, ta bayyana cewa ’yan Najeriya miliyan 11 ne ya zuwa suka ci gajiyar Shirin Tallafa wa da Ci gaban Al’umma (CSDP) a jihohi 29 inda aka kashe Dala miliyan 415 a kai.

Ta bayyana cewa ta hanyar shirin an gina azuzuwa guda 5,764 da cibiyoyin kiwon lafiya guda 1,323 a wasu kananan ayyuka guda 4,442 inda wasun aka yi musu kwaskwarima yayin da aka gudanar da wasu kananan ayyukan guda 16,166 a kauyuka 5,664.

Sun ta rahoto cewa ministar ta fadi hakan a ranar Laraba a Abuja yayin wani taro kan shirin na CSDP, inda ta ce an faro shirin ne tun a 2009, sannan ya kunshi harkokin rayuwar yau da kullum guda takwas — ilimi da kiwon lafiya da ruwa da sufuri da lantarki da zamantakewar yau da kullum da muhalli da raya karkara.

KU KARANTA: Dalilin da Buhari da APC suka gaza a cikin shekara hudun farko — Shugaban Majalisar Dattijai Ahmed Lawan

Tallafin rayuwa: Mun kashe wa ’yan Najeriya miliyan 11 Dala miliyan 415 – Minista
Tallafin rayuwa: Mun kashe wa ’yan Najeriya miliyan 11 Dala miliyan 415 – Minista
Asali: Instagram

DUBA NAN: Najeriya ta talauce, wajibi ne mu cigaba da karban bashi: Shugaban Majalisa

Ministar.tace:

“Shirin ya faro ne a 2009, inda ya kara samun kudin gudanarwa har guda biyu jimallarsa ya tashi Dalar Amurka miliyan 415,."
Cikin shekara fiye da 11 da shirin ya yi, ya zama guda cikin gishikan aiwatar da tsare-tsare da manufofin gwamnatin tarayya na tallafa wa jama’a karkashin ma’aikatar da nake kula da ita.
‘’Wannan shiri ne da ke kula da bukatun talaka da gajiyayyun mutane tare da samar musu da tallafin ababen ci gaban rayuwa domin su shawo kan muhimman bukatunsu na rayuwar yau da kullum.
“Ta hanyar amfani da wannan dabarar shirin na CSDP ya aiwatar da kananan ayyuka a kauyuka da dama cikin kananan hukumomi 543 a jihohi 29 tare da babbabn birnin tarayya. Wannan yana daidai da kashi 70% na adadin kananan hukumomin tarayyar Najeriya.

Sadiya ta kara da cewa gano al’ummomin da suka fi fama da talaucin ta hanyar amfani da Taswirar Fatara da kowace jihar da ke cikin shirin ta amince da shi da ma babban birnin tarayya.

Za'a dauki sabbin matasan N-Power

Ma'aikatar jin ƙai da walwala ta bayyana cewa aƙalla mutum 550,000 ne suka tsallake matakin tantancewa daga cikin mutum 1.8 miliyan da suka nemi gurbin aiki a shirin npower.

Hajiya Sadiya Farouq, ministar ma'aikatar jin kai da walwala, ita ce ta bayyana haka a wani taron manema labarai ranar Talata a Abuja, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel