Cikakken masoyin Shugaban kasa ya rubuta littafi sunkutum a kan rayuwar Buhari

Cikakken masoyin Shugaban kasa ya rubuta littafi sunkutum a kan rayuwar Buhari

  • Abdullahi Haruna da aka fi sani da 'Haruspice' ya wallafa littafin ‘The Buhari in Us’
  • Haruspice ya rubuta wannan littafi saboda kaunar da yake yi wa Shugaban Najeriya
  • Mawallafin ya ce tun a 2003 ya fara sha’awar halaye da akidun Muhammadu Buhari

Legit.ng ta samu halartar bikin kaddamar da littafin da shahararren marubuci kuma ‘dan jarida, Abdullahi Haruna 'Haruspice', ya wallafa, ‘The Buhari in Us’.

An kaddamar da wannan littafi a cibiyar gidan soja na Nigerian Army Resource Centre da ke birnin tarayya Abuja a jiya ranar Talata, 22 ga watan Yuni, 2021.

Abdullahi Haruna wanda aka fi sani da Haruspice ya na cikin ‘ya ‘yan jam’iyyar APC, ya ce ya rubuta littafin a 2018, amma sai a shekarar banan nan ya fito.

KU KARANTA: Abin ya jawo wa Buhari matsala a 2015 - Ahmad Lawan

Da bazar Buhari mu ke rawa – Haruspice

Matashin marubucin gawurtaccen masoyin shugaban kasa Muhammadu Buhari ne, ya ce tun ya na sakandare a shekarar 2003, ya fara sha'awar halayen Buhari.

“An rubuta wannan littafi da aka kaddamar yau a shekarar 2018. Amma saboda hali na lokaci da rayuwa, sai a yau aka iya fito da shi gaban jama’a.” inji Haruspice.

Mawallafin ya ce: “A dade ana yin abu shi ne yake bayyana wanene mutum; idan ba za ka iya bada kaimi wajen ganin burinka ya kai ga ci ba, da fari kar a soma.”

“Tun 2003 na kankame akida da halayyar Muhammadu Buhari. Da bazarsa na ke rawa, na kuma yi ta tallata akidunsa na kwarai da ake gani a salon shugabancinsa.”

KU KARANTA: Buhari: Hana Twitter da aka yi daidai ne – ‘Dan Majalisar Daura

The Buhari in Us ya fito
The Buhari in Us Hoto: HARUSPICE
Asali: Facebook

“Kamar yadda kuka sani, abubuwa da yawa sun faru, an samu sauyi a tafiyar, amma makasudin na nan.” Marubucin ya yi wa jama'a godiya a shafinsa na Facebook.

Duk wannan kokari da mawallafin ya yi, ya ce daga wancan lokacin da ya fara kaunar shugaban Najeriyar har zuwa yau, sau daya rak kurum ya taba haduwa da shi.

Wadanda aka gayyata zuwa wajen taron sun hada da; Gwamna Yahaya Bello, Ministan Abuja, Sanata Muhammad Sani Musa, Rotimi Amaechi, Ramatu Tijjani Aliyu.

A ranar Talata aka ji cewa Jami’ar Cavendish ta Uganda ta zabi Dr. Goodluck Jonathan a matsayin Shugabanta. Jami’ar ta na cikin makarantun da ake ji da su a Afrika.

Goodluck Jonathan zai maye gurbin tsohon shugaban Zambiya, marigayi Keneth Kauda. CUU ta bada wannan sanarwa ne a shafinta na Facebook a farkon makon nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel