An bayyana Jihar Arewa a matsayin wanda ta fi kowa yawan Talakawa, Jihar Kudu ta zo a karshe

An bayyana Jihar Arewa a matsayin wanda ta fi kowa yawan Talakawa, Jihar Kudu ta zo a karshe

  • Alkaluma sun nuna 10% na Talakawan Najeriya duk suna zaune a jihar Zamfara
  • Hukumar NASSCO ta yi bincike, ta gano Talakawa miliyan 35.2 su ke kasar nan
  • NSR ta ce kusan miliyan 4 daga cikin wadannan marasa karfi suna jihar Zamfara

Zamfara ta zo ta farko a matsayin Jihar da ta tara yawan talakawa da masu karamin karfi a fadin kasar nan, jaridar Punch ta fitar da wannan rahoto.

Rahoton da aka fitar a ranar 22 ga watan Yuni, 2021, ya bayyana cewa akwai talakawa miliyan 3.8 a jihar.

Bayanan da aka samu daga hukumar National Social Registry mai tattara alkaluma ya nuna akwai talakawa 3,836,484 a gidaje 825,337 a jihar Zamfara.

KU KARANTA: Kungiya ta tattara sunayen mutanen da aka kashe a Najeriya

Wani babban jami’in hukumar da ke aiki a ofishin bada agaji ga marasa galihu da ke Abuja, Joe Abuku, ya fitar da wannan alkaluma da aka tuntube shi.

Aikin hukumar NASSCO

An kafa hukumar NASSCO ne a shekarar 2016 tare da hadin-kan gwamnatin tarayya da bankin Duniya domin a rage talaucin da ake fama da shi a kasar nan.

NSR ce wanda NASSCO ta ba nauyin tattara bayanan marasa karfi da galihu, ta haka ne hukumar za ta dauki mataki game da yadda za a fito da su daga kangi.

Alkaluman na NASSCO sun nuna zuwa ranar 31 ga watan Mayu, 2021, an samu talakawa tubus har 35,267,966, wadanda su na rayuwa ne rai hannun Allah.

KU KARANTA: Maigida ya yi ram da Amininsa a gidansa tsirara a Katsina

NRPGS
Kwamitin yaki da talauci a Najeriya Hoto: @ Femi Adesina
Asali: Facebook

Jihohin da suka fi fama da talauci

Yayin da Zamfara ta tattara kusan kashi 11% na wadannan marasa karfi, jihar Ekiti ce ta zo ta karshe, talakawa 94,923 kurum aka samu daga gidaje 32,949.

Ripple Nigeria ta tabbatar da rahoton, ta ce a Kebbi an samu talakawa 3,745,427 a gidaje 807,261, jihar Kano ta shiga sahun da talakawa 2,697,160 a gidaje 542,764.

A Borno an samu 157,841 zaune a gidaje 30,957, yayin da a Ondo aka samu mutane 171,119 cikin fatara. Akwai talakawa 511, 353 da 1, 848, 767 a Legas da Abuja.

A makon nan ne aka ji cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da wani kwamiti da zai yi aikin ceto mutum miliyan 100 daga bakin talauci a Najeriya.

Ana so wannan kwamiti da yake karkashin mataimakin shugaban kasa, Farfesa, Yemi Osinbajo, ya ceto mutum miliyan 100 daga halin talauci nan da shekara goma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel