Buhari ya rantsar da ‘yan kwamitin da za su ceto mutum miliyan 100 daga bakin talauci
- Muhammadu Buhari ya kaddamar da kwamitin NPRGS a fadar Aso Villa
- Ana so wannan kwamiti zai ceto mutum miliyan 100 daga fatara a Najeriya
- Shugaba Buhari ya ce Gwamnatinsa za ta yi koyi ne da abin da Indiya tayi
A ranar Talata, 22 ga watan Yuni, 2021, Shugaba Muhammadu Buhari, ya kaddamar da kwamitin da aka ba alhakin rage talauci da bunkasa tattalin Najeriya.
Ana so wannan kwamiti da yake karkashin mataimakin shugaban kasa, Farfesa, Yemi Osinbajo, ya ceto mutum miliyan 100 daga halin talauci a fadin kasar.
Mai girma Muhammadu Buhari ya yi alkawari gwamnatinsa ta tsara dabarun da za ta bi domin ceto mutanen da talauci ya yi daurin goro nan da shekaru goma.
KU KARANTA: AfDB za ta kashe N180b wajen shimfida titi daga Najeriya zuwa Kamaru
Mai magana da yawun bakin shugaban kasa Femi Adesina, ya bayyana wannan a wani jawabi da ya fitar.
Da yake magana a bikin rantsar da wannan kwamiti, jaridar Punch ta ce shugaban kasar ya bayyana dabarar da kwamitin NPRGS za ta bi wajen yin wannan aiki.
Muhammadu Buhari ya ke cewa an soma aikin ne tun Junairun 2021 lokacin da ya bukaci majalisar masu ba shi shawara kan tattalin arziki su yi maganin fatara.
Premium Times ta rahoto shugaban Najeriyar ya na cewa za ayi maganin duk kura-kuren da aka yi a baya, a fito da tsarin da zai azurta miliyoyin mutanen da ke kasar nan.
KU KARANTA: Idan Buhari ya tafi akwai kura a APC - Lawan
Najeriya za ta yi koyi da Indiya
Ya ce: “Idan Indiya za ta iya kubuto da mutane miliyan 271 daga talauci tsakanin 2006 da 2016, tabbas Najeriya za ta iya ceto mutum miliyan 100 a shekaru goma.”
“Abin farin cikin shi ne mun riga mun fara wannan aiki, amma muna bukatar mu shawo kan kalubalen nawan da mu ke yi wajen dabbaka shirin namu.” Inji sa.
‘Ya ‘yan wannan kwamitin
Wadanda suke cikin wannan kwamiti sun hada da sakataren gwamnatin tarayya, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, da gwamna daga kowane bangare.
Akwai gwamnonin Delta, Ekiti, Nasarawa, Sokoto, Borno da na Ebonyi. Sai Ministocin tattalin arziki, aikin gona, kwadago, agaji, ilmi, kiwon lafiya, da masana’antu.
A jiya aka ji cewa shugaba Muhammadu Buhari ya halarci gangamin da matasan APC suka kira, inda ya yi wa matasan huduba, su tashi su gyara Najeriya domin gaba.
Shugaban kasar ya ce maganar cewa ana maida wasu saniyar ware a mulkinsa, ba gaskiya ba ne.
Asali: Legit.ng