Kungiya ta tattara sunayen mutum kusan 1,500 da aka kashe a Najeriya a shekara 10

Kungiya ta tattara sunayen mutum kusan 1,500 da aka kashe a Najeriya a shekara 10

  • #SecureOurLives ta na tara sunayen mutanen da aka hallaka a Najeriya
  • Kungiyar ta iya samun bayanin mutum 1, 499 da suka mutu a shekara 10
  • A Najeriya babu wata rajista da ke kunshe da sunan wadanda suka mutu

Gamayyar kungiyoyi masu zaman kansu a karkashin #SecureOurLives, suna tara sunayen wadanda aka hallaka a ‘yan shekarun bayan nan a Najeriya.

Jaridar Daily Trust ta ce #SecureOurLives ta kinkimo wannan aiki ne domin a samu inda ake adana sunayen wadanda matsalar rashin tsaro ta ci a fadin kasar.

An samu sunayen mutane 1, 499 a rajista

An soma wannan aiki ne a watan Afrilun 2021, daga wancan lokaci zuwa yanzu, an samu sunayen mutane 1, 499 da aka hallaka a sanadiyyar matsalar tsaro.

KU KARANTA: Motar mai ta jawo gobara a titin Legas, wuta ya ci motoci

A yau ranar Talatar nan, 22 ga watan Yuni, 2021, ake sa ran fito da sunayen dinbin mutanen da suka riga mu gidan gaskiya a cikin shekaru goma da suka wuce.

Abin da ya sa aka soma wannan aikin

Wata daga cikin ‘ya ‘yan wadannan kungiya, Buky Williams, ta bayyana manufars aikin da suke yi.

Ayisha Osori ta ce abin mamaki ne ace kasa irin Najeriya ba ta da wani rajista inda ake tattara sunayen mutanen da aka kashe, ko kuma rikici ya rutsa da su.

Misis Osori ta ce: “Mun lura babu inda ake ajiye sunayen wadanda matsalar tsaro da rikice-rikice ya rutsa da su, saboda haka mu ka yi tunanin a kirkiri wani.”

“Zuwa Oktoba, za mu tattara duk rashin da mu ka yi, mu tara sunayen da muka iya tabbatarwa.”

KU KARANTA: Masu zanga-zangar 'Buhari sai ya tafi' sun tare hanya

New IGP
Sabon IGP da Yemi Osinbajo Hoto; Facebook
Asali: Twitter

Wannan kungiya ta ce ta na kan aikin tantance sunayen daruruwan mutanen da aka kashe a rikicin ‘Yan shi’a da sojoji da kuma rikicin kudancin jihar Kaduna.

Za a ajiye wannan rajista da aka hada a yanar gizo ta yadda kowa zai iya gani. Hukumomin kasar waje irinsu ACLED sun bada gudumuwa a wajen gagarumin aikin.

A wajen taron kungiyar ECOWAS da ake yi a kasar Ghana, shugaban bankin cigaban Afrika, AfDB, Akinwumi Adesina ya ce ya kawowa Najeriya kwangilar $430m.

Kasashen yammacin Afrika su na cin moriyar AfDB a karkashin tsohon Ministan gona, Dr. Akinwumi Adesina ya ce za a gama titin Enugu zuwa Kamaru a bana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel