Dr. Goodluck Jonathan ya samu babban mukami a kasar Afrika shekaru 6 da barin karagar mulki

Dr. Goodluck Jonathan ya samu babban mukami a kasar Afrika shekaru 6 da barin karagar mulki

  • Jami’ar Cavendish ta Uganda ta zabi Goodluck Jonathan a matsayin Shugaba
  • Rahotanni sun ce jami’ar tana daya daga cikin manyan jami’o’i a nahiyar Afirka
  • Dr. Goodluck Jonathan zai canji tsohon Shugaban kasar Zambia, Keneth Kauda

A ranar Talatta, 22 ga watan Yuni, 2021, mu ka samu rahotanni daga VOA Hausa cewa tsohon shugaba, Dr. Goodluck Ebele Jonathan, ya samu mukami.

Kamar yadda rahoton ya bayyana, tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan ya zama shugaban jami’ar Cavendish da ke kasar Uganda ta CUU.

KU KARANTA: Jonathan ya zama Jakadan ECOWAS na musamman

Kujera a Jami’ar CUU

Dr. Goodluck Ebele Jonathan wanda ya bar kujerar shugaban kasa a watan Mayun 2015 zai dare kujerar ‘Chancellor’ a wannan jami’a da ke kasar Uganda.

Jaridar Daily Post ta ce jami’ar ta bada wannan sanarwa ne a shafinta na Facebook a makon nan.

Sanarwar take cewa: “Barka da zuwa Goodluck Jonathan, yayin da ka amince ka zama shugaban jami’ar CUU. Mu na sa ran aiki da kai, domin samun nasara.”

“Yanzu jami’ar Cavendish ta shigo gari.” Makarantar ta ci burin kai ga ci a karkashin Dr. Jonathan.

KU KARANTA: Jonathan zai shiga Kasar Mali da sauran Shugabannin ECOWAS

Dr. Goodluck Jonathan
Goodluck Jonathan a Ghana Hoto: www.voahausa.com
Asali: UGC

Jami’ar Cavendish watau CUU ba ta gwamnati ba ce, ta kudi ce, ta na cikin manyan jami’o’in da suke tashe a halin yanzu a fadin kasashen da ke nahiyar Afrika.

An kafa wannan jami’a ne a 2008, sannan ta fara yaye dalibanta a 2011. Kafin yanzu marigayi Kenneth Kaunda wanda ya mutu kwanan nan shi ne shugabanta.

Farin jini bayan barin mulki

Tun bayan barinsa karagar mulki yake samun mukamai da kyaututtuka a Duniya, wannan sabuwar kujera ta na cikin mukaman da Jonathan ya samu a ketare.

Daga 2015 zuwa yanzu, Goodluck Jonathan ya zama Jakadan kungiyar ECOWAS wajen sasanta rikicin da ya barke a kasar Mali, kuma ya yi aikin zabukan kasashe.

A watan da ya wuce, Dr. Jonathan ne ya shiga-ya fita har sai da Sojojin tawaye suka fito da Shugabannin Mali da suka tsare bayan wani juyin-mulki da aka yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel