Hana Twitter: ‘Dan Majalisar Daura ya na goyon-bayan Buhari, ya ce Twitter ba abinci ba ne

Hana Twitter: ‘Dan Majalisar Daura ya na goyon-bayan Buhari, ya ce Twitter ba abinci ba ne

  • Hon. Fatuhu Muhammad ya ce an yi daidai da aka hana Twitter aiki a kasar nan
  • ‘Dan Majalisar ya yi magana wajen sauraron zaman da aka shirya a Majalisa
  • Muhammad yake cewa ya kamata gwamnati ta rika sa ido a kafofin sadarwa

‘Dan majalisa mai wakiltar mazabar Daura, Sandamu da Maiadua, Fatuhu Muhammad, ya nuna goyon-bayansa ga gwamnatin tarayya a kan hana Twitter.

Jaridar Premium Times ta ce Honarabul Muhammad ya mike a gaban majalisar wakilan tarayya a ranar Talata, 22 ga watan Yuni, 2021, ya bayyana matsayarsa.

Zaman da majalisar tarayya ta shirya

‘Dan majalisar ya yi wannan jawabi ne a wajen zaman da aka shirya domin kwamitin majalisar dattawa da ta wakilai su saurari korafai daga bakin jama’a.

Kwamitin yada labarai da wayar da na tsaro, shari’a da kasuwanci sun kira zama na musamman, inda aka tattauna a kan matakin haramta Twitter aiki a Najeriya.

KU KARANTA: Buhari: Za mu yi koyi da Indiya, mu azurta mutane miliyan 100

Twitter ba abinci ba ne

A ra’ayin, Fatuhu Muhammad, kafofin sada zumunta na zamani ba abinci ba ne da ba za a iya rayuwa babu su ba, don haka ya nuna za a iya haramta su.

Fatuhu Muhammad wanda ya na cikin duka wadannan kwamitoci a majalisa, yake cewa komai za ayi, ya kamata a fara la’akari ne da al’ummar Najeriya.

“Don Allah menene kafar sada zumunta? Mu na cin dandalin sada zumuntan nan ne? Mu koma kan arzikin da mu ke da shi, mu ci moriyarsu.” Inji Muhammad.

‘Dan majalisar na Daura, Sandamu da yankin Maiadua, ya cigaba da cewa: “Mu ajiye wannan batu a gefe guda (haramta Twitter), mu fuskanci ainihin matsalolinmu."

KU KARANTA: Lissafi ya fara canzawa a gidan APC a wajen takarar Shugabancin Jam’iyya

Shugaban Majalisar Wakilai
'Dan Majalisar Wakilai, Fatuhu Mohammed Hoto: House of Reps
Asali: UGC

“Abokan aikina sun yi magana a madadin mutanen mazabarsu. Idan zan yi magana a madadin mutanena, zan hada har da shugaban kasa, domin shi ya zabe ni.”

“Da ace ba a hana Twitter ba, da cin mutuncin da za a rika yi mana ya wuce nan. Mu fada wa kanmu gaskiya, idan ina duba Twitter na kan ji takaicin matasanmu.”

NNN ta ce Honarabul din yace dole gwamnati ta rika bibiyar abubuwan da ake yi a wadannan kafofi, ya ce an dakatar da aikinsu ne saboda a tsare martabar Najeriya.

Kafin zaben 2019 an ji cewa mutane sun yi ta babatu a kan yunkurin APC na neman mikawa ‘Dan uwan Shugaban kasar tikitin Majalisa, wasu sun rika nuna ba su yarda ba.

Fatuhu Muhammad yanzu ya na wakiltar mahaifar shugaban kasa Muhammadu Buhari, sannan ya na cikin manyan kusoshin jam’iyyar APC mai mulki a jihar Katsina.

Asali: Legit.ng

Online view pixel