Dr. Goodluck Jonathan ya zama Jakadan ECOWAS na musamman a kasar Mali

Dr. Goodluck Jonathan ya zama Jakadan ECOWAS na musamman a kasar Mali

- Goodluck Ebele Jonathan ya samu kujera Jakada a kungiyar ECOWAS

- Kungiyar kasashen yammacin Afrikan ta aikowa Jonathan takarda a ranar Talata

- Jean-Claude Kassi Brou ya sa hannu a wasikar tsohon shugaban na Najeriya

A yunkurin da ake yi na kawo karshen matsalar siyasa da zamantakewar da kasar Mali ta shiga, tsohon shugaban kasan Najeriya, Goodluck Jonathan, ya zama jakada zuwa kasar.

Dr. Goodluck Ebele Jonathan zai yi aikin kawo zaman lafiya a kasar Afrikan bayan da a jiya kungiyar ECOWAS ta nada shi a matsayin Jakadan ta na musamman.

A ranar Talata, 14 ga watan Yuli, ECOWAS ta tabbatar da Goodluck Jonathan a matsayin babban Jakadan kungiyar kasashen yammacin Afrika da zai kawo zaman lafiya a kasar Mali.

Daga cikin aikin da tsohon shugaban kasar zai yi, zai gana da shugabannin Mali, Ibrahim Boubacar Keita, fitaccen ‘dan shugaban kasar da manyan ‘yan siyasar adawa.

Haka zalika Dr. Goodluck Jonathan zai zauna da kungiyoyi masu zaman kansu da malaman addini duk da nufin ganin an kwantar da tashin-tashinar siyasar da ake nema a jefa yankin.

KU KARANTA: Dasuki ya yi wa APC aiki lokacin da ya ke tare da Jonathan?

Dr. Goodluck Jonathan ya zama Jakadan ECOWAS na musamman a kasar Mali
Dr. Goodluck Jonathan
Asali: Twitter

Legit.ng ta samu labarin wannan aiki da aka ba Goodluck Ebele Jonathan ta wasikar da ECOWAS ta aiko masa wanda shugabanta, Jean-Claude Kassi Brou ya sa wa hannu.

Wasikar ta na cewa: “Ganin matsayin ka na tsohon shugaban kasar Najeriya da irin rawar da ka taka a gwamnatinka na kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankinmu, bayan tattaunawa da shugaban kungiyar, mai girma Issoufou Mahamadou, shugaban kasar Nijar, ina mai samun alfarmar shaida maka matakin ECOWAS na nada ka a matsayin Jakada na musammana domin shawo kan rigimar siyasa da zamantakewar kasar Mali.”

Kasar Mali ta tsinci kan ta a wani mummunan yanayi bayan zabukan da aka yi a watannin Maris da Afrilu, inda jama’a su ke kara nuna rashin goyon baya ga gwamnati mai ci a kasar.

Ana zargin gwamnatin Ibrahim Boubacar Keita da gaza kawo karshen rashin tsaro da matsalar tattalin arziki da ake fama da shi, wannan ya jawo ake kiran shugaban kasar ya yi murabus.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel