ECOWAS: Jonathan zai shiga Kasar Mali da sauran Shugabannin Yankin Afrika

ECOWAS: Jonathan zai shiga Kasar Mali da sauran Shugabannin Yankin Afrika

Rahotanni daga AFP sun ce tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan, zai jagoranci wasu shugabannin Afrika ta yamma zuwa kasar Mali.

Dr. Goodluck Jonathan da sauran shugabannin Afrikan za su kai ziyara zuwa kasar da aka yi juyin-mulki ne a ranar Asabar, 22 ga watan Agusta, 2020.

A makon nan sojoji su ka tsare shugaban kasa Ibrahim Keita da sauran manyan jami’an gwamnatin Mali wanda su ka hada da Firayim minista Boubou Cisse.

Wannan ya sa shugaba Ibrahim Keita ya bada sanarwar murabus a ranar Laraba, Keita ya ce ya yi hakan ne domin a gujewa zubar da jinin al’umman kasar.

Goodluck Jonathan wanda ya ke ta kai-komo wajen ganin an samu zaman lafiya a kasar Mali zai sake kai wata ziyara, kwanaki hudu da kifar da gwamnati mai-ci.

KU KARANTA: Mali: Wanene Shugaba Ibrahim Keita

ECOWAS: Jonathan zai shiga Kasar Mali da sauran Shugabannin Yankin Afrika
Jonathan a Kasar Mali kwanaki
Asali: Facebook

Dr. Jonathan zai kai wannan ziyara ne a karkashin kungiyar ECOWAS tare da wasu shugabanni na kasashen Afrika ta yamma wadanda su ke makwabtaka da Mali.

A ranar Alhamis, ECOWAS ta bada sanarwar cewa za ta tada tawaga ta musamman da za su tafi Mali da nufin ganin tsarin mulkin farar hula ya cigaba da aiki.

Kamar yadda rahoton ya nuna, burin wannan tawaga ta ECOWAS shi ne dawo da Ibrahim Keita kan mulki. Har yanzu Keita ya na tsare a hannun 'yan tawayen sojoji.

Wadanda za su takawa Jonathan baya su ne shugabanni 14 na yankin Nahiyar. Ana sa rai zuwa safiyar ranar Asabar, tawagar ta isa babban birnin Mali na Bamako.

Tawagar ECOWAS ta Jonathan za ta gana ne da Assimi Goita, shugaban sojojin da su ka hambarar da gwamnati. Goita ya bada sanarwar zama sabon shugaban hafsun soji.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel