AfDB za ta kashe Naira Biliyan 180 wajen shimfida shararren titi daga Najeriya har Kamaru

AfDB za ta kashe Naira Biliyan 180 wajen shimfida shararren titi daga Najeriya har Kamaru

  • AfDB ya yi alkawarin kammala titin Enugu zuwa Bameda a shekarar bana
  • Shugaban AfDB ya sha wannan alwashi a wajen taron ECOWAS jiya a Ghana
  • Akinwunmi Adesina ya lissafo ayyukan da AfDB ya kawo Yammacin Afrika

Bankin cigaban Afrika, AfDB, ya ce za a kammala aikin kwangilar babban titin nan da zai hada Najeriya da kasar Kamaru a cikin shekarar nan ta 2021.

Premium Times ta rahoto shugaban bankin nahiyar, Akinwunmi Adesina, ya na wanan bayani a wani jawabi da ya yi a ranar Litinin, 21 ga watan Yuni, 2021.

Da yake magana a taron shugabanni da gwamnatocin kungiyar ECOWAS, Dr. Akinwunmi Adesina yace aikin ya na cikin romon da aka kawo yammacin Afrika.

KU KARANTA: An rufe makarantu a Kebbi saboda satar dalibai

Titin Enugu – Bamenda zai ci $430m

Dr. Adesina ya ce wannan titi zai taso daga Enugu, sannan ya tike a Bamenda a kasar Kamaru. Kwangilar za ta ci Dala miliyan 430, kimanin Naira biliyan 180.

Shugaban bankin na AfDB ya bada tabbacin cewa bankin na kokarin duba yiwuwar aikin titin Najeriya zuwa kasar Ivory Coast da zai ratsa Abidjan zuwa Legas.

Jaridar The Cable ta rahoto Adesina ya na cewa wannan babban titi zai taimaka wajen safarar 85% na kayan da ake fatauci tsakanin kasashen yammacin Afrika.

Dr. Akinwunmi Adesina yake cewa: “Muna sa ran a soma aikin titin nan da watanni 24.”

KU KARANTA: Abin da ya sa muke karbo bashi - Ministan Buhari

Shugaban AfDB
Dr. Akinwumi Adesina Hoto: www.dailytimes.ng
Asali: UGC

Sauran ayyukan da AfDB yake yi a Afrika ta yamma

A cewar Adesina, bankin AfDB yana kashe makudan kudi a yammacin Afrika a karkashinsa, ya ce an ware wa yankin abin da ya kai fam Dala biliyan 16 a yanzu.

Kudin da AfDB ta ke batar wa a yankin ya nunku biyu a cikin shekaru biyu daga $2bn zuwa $4bn.

Daga cikin manyan ayyukan da aka kawo akwai gadar Senegambia da ta hada Sanagal da Gambia. Sannan ana kashe kudi wajen inganta tashar Lome a Togo.

Bankin ya gyara hanyar Bamako-San Pedro da titin Ouagadougou zuwa Lome. Sannan titi zai hada Sierra Leone, Guinea da Laberiya, ga kuma titin Guinea-Bissau.

A shekarar bara ne aka ji cewa an sake zaben Dr. Akinwunmi Adesina a matsayin shugaban bankin cigaban nahiyar ta Afrika, AfDB, wanda shi ne karonsa na biyu.

Kwamitin gwamnonin bankin ne suka sake zaben Adesina duk da zargin da ke kansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel