Kowa na ka: Akwai adalci a rabon kujeru da ayyukan da nake yi a mulkina inji Buhari

Kowa na ka: Akwai adalci a rabon kujeru da ayyukan da nake yi a mulkina inji Buhari

  • Shugaban kasa ya yi magana a wajen gangamin matasan da APC ta shirya
  • Muhammadu Buhari ya yi kira ga matsa su tashi tsaye wajen cigaban kasa
  • Boss Mustafa ne ya wakilci Shugaba Muhammadu Buhari wajen gangamin

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ya na yin adalci tare da tafiya da kowa wajen rabon mukamai, manfofin gwamnati da ayyukan da yake yi.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa shugaban kasar ya yi magana a wajen taron matasa na kasa da jam’iyyar APC ta shirya a ranar Litinin a birnin Abuja.

Buhari ya ce: “Babu wani bangare na kasar nan da bai ci moriyar ayyukan more rayuwa, harkar noma, da gudumuwar tattalin arziki na gwamnatin APC ba.”

KU KARANTA: An gano yadda kungiyar IPOB ta ke horas da sojojinta

Boss Mustafa ya wakilci Shugaban Najeriya a taron

Muhammadu Buhari ta bakin wakilinsa, ya ce gwamnatinsa ta kai wa kowane yankin kasar ayyukan cigaba da tsare-tsaren da mutanensu suka fi bukata.

The Cable ta ce sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ne ya wakilci shugaban kasar a taron.

Da yake jawabi a madadin mai girma shugaban Najeriya, Boss Mustapha yace gwamnatinsa da gaske ta ke yi wajen kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali.

KU KARANTA: Mu na tara sunayen mutanen da suka mutu a sanadiyyar rashin tsaro - Kungiya

Muhammadu Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Shawarar Shugaban Najeriya ga matasan kasar nan

Har ila yau, a jawabin na sa, Muhammadu Buhari ya yi kira ga matasan kasar nan, su yi kokarin kawo gyara ta yadda za su ci moriyar Najeriya a nan gaba.

“Ka da ku karaya, ka da ku gajiya, a wajen kokarin kawo cigaban kasa. Ku tuna cewa ba mu da wata kasa sai Najeriya. Nauyinmu ne mu dage wajen cigabanta.”

“Na fada a ‘yan kwanakin nan sau da yawa, duk wani mugun mutum da ya dauki makami ya na tada zaune tsaye a kasar nan, zai dandana kudarsa.” Inji Buhari.

Ana zargin gwamnatin Muhammadu Buhari da fifita mutanen Arewa wajen bada mukaman gwamnati, shugaban kasar ya musanya wannan zargi mai nauyi.

An ji cewa kungiyar SERAP ta na karar Gwamnatin Tarayya a wani kotu a Abuja. Lauyoyin kungiyar sun shigar da kara mai lamba FHC/ABJ/CS/496/2021.

SERAP ta shigar da karar gwamnatin Najeriya ne a kan haramtawa ‘yan jarida amfani da Twitter. Kungiyar ta na ganin wannan matakin ya saba wa dokar kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel