Korar ma'aikata: El-Rufai ya jefa al’ummar Kaduna a halin wayyo Allah inji Ramalan Yero
- Mukhtar Ramalan Yero ya soki manufofin Gwamna Malam Nasir El-Rufai
- Tsohon Gwamnan ya ce Magajinsa ya gaza ya kawo tsaro da saukin rayuwa
- Yero ya kushe ayyukan da ake cewa Gwamnatin APC ta na yi a cikin Birane
Alhaji Mukhtar Ramalan Yero wanda ya rike kujerar gwamnan jihar Kaduna tsakanin 2012 da 2015, ya yi tir da gwamnati mai-ci ta Malam Nasir El-Rufai.
A wata hira ta musamman da ya yi da BBC, Mukhtar Ramalan Yero, ya bayyana cewa magajinsa, Nasir El-Rufa'i, ya gaza wajen samar da zaman lafiya a Kaduna.
Sallamar ma'aikatan gwamnati bai dace ba - Yero
A ra’ayin tsohon gwamnan na PDP, matakin da gwamnatin Nasir El-Rufai ta dauka na korar ma'aikata, ya sake jefa talakawa cikin halin wayyo Allah a jihar.
KU KARANTA: El-Rufai ya ja-kunnen masu toshe tituna a Kaduna
Tsohon gwamnan ya musanya rade-radin da ake yi na cewa gwamnatinsu ta jam’iyyar PDP ta rika yin arin-gizon ma’aikata a Kaduna, ya ce sam ba su yi haka ba.
Mukhtar Ramalan Yero ya zargi gwamna Nasir El-Rufa'i da jefa al’umma a kangi, ya ce matakin ya bar makarantu da asibitoci suna fama da karancin ma’aikata.
Mukhtar Ramalan Yero wanda ya yi kusan shekaru uku a mulki ya ce bai kamata gwamnati ta rika sallamar ma’aikata ba, domin dama can ba riba ta fito nema ba.
Gwamnatin El-Rufai ta gaza cika alkawuranta
A na sa ra’ayin gwamnatin APC ta na bakin-kokarinta, amma ya ce: “Dole ne ace gwamnati ta gaza a wurare daban-dabam, kuma dole a saurari korafin jama’a.”
KU KARANTA: Gwamnonin APC sun rungumi wani Sanata a takarar Shugaban jam'iyya
“Ta yi kamfe sosai a kan batun tsaro, yanzu sha’anin tsaron ba gyaruwa ya ke yi ba, sai dai ma kara lalacewa, mutane na cikin wani hali, gwamnati ta gaza kwarai.”
A game da abubuwan more rayuwar da ake gani a birane, Yero ya fada wa BBC: “Gwamnatinmu tayi la’akari da kananan hukumomi 23, a ko ina PDP ta yi aiki iri-iri.”
“Duk idan aka hada tsawon titunan da ake yi yanzu, ba su kai tsawon hanyar Yakowa da muka yi ba.”
A karshen makon da ya gabata ne hukumar INEC ta sanar da sakamakon zaɓen cike gurbin da ta gudanar a mazaɓar Sabon gari, jihar Kaduna, inda PDP ta samu nasara.
Baturen zaɓen Dr. Muhammed Musa, ya bayyyana ɗan takarar PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓe. Hakan na zuwa ne bayan karbe kujerar Rt. Hon. Aminu Shagali.
Asali: Legit.ng