‘Dan takarar da ba ayi tunani ba zai bada mamaki a tseren zama Shugaban Jam'iyyar APC

‘Dan takarar da ba ayi tunani ba zai bada mamaki a tseren zama Shugaban Jam'iyyar APC

  • Rahotanni sun ce zaben shugabannin jam’iyyar APC da za ayi, zai iya ba kowa mamaki
  • Za a kawo ‘dan takara daban daga cikin wadanda suke harin kujerar shugaban jam’iyya
  • Hankali ya karkata a kan wani Sanata daga jihar Neja a maimakon sauran da ake tunani

Rahotanni daga jaridar Leadership sun bayyana cewa akwai yiwuwar wani ‘dan takara dabam daga gefe guda ya zama shugaban jam’iyyar APC na kasa.

Alamu suna nuna jiga-jigan jam’iyyar APC suna goyon bayan wani ‘dan takara daga jihar Neja domin ya dare kujerar da Adams Oshiomhole ya bari a bara.

Wani kusa a jam’iyyar ta APC ya shaida wa ‘yan jarida cewa akwai wani ‘dan takara da ya bazo wuta daga baya, yanzu haka Sanata ne mai-ci a jam'iyyar APC.

KU KARANTA: Watakila APC za ta yi zaben shugabanni a watan Oktoba

Wanda ba a sani ba zai bada mamaki

Sanatoci uku ne ake da su daga Neja kamar kowace jiha. Sanatocin su ne; Bima Muhammad Enagi, Abdullahi Aliyu Sabi da kuma Mohammed Sani Musa.

Yanzu haka akwai masu neman kujerar shugaban APC na kasa biyu daga jihar, daga ciki akwai Sanata da yake majalisar dattawa da wani tsohon Ministan kasar.

Majiyar ta ce an fi ganin cewa wannan ‘dan majalisar tarayyar zai kai labari idan aka shiga takara.

“Ku sani kuma akwai wasu tsofaffin gwamnoni biyu daga Arewa maso tsakiya da suke sha’awar wannan kujera, daya ya na Benuwai, guda ya na Nasarawa.”

KU KARANTA: 2023: Kila da matsala a APC idan Buhari ba ya nan - Lawan

Majalisar Dattawa
Majalisar Dattawan Najeriya Hoto: Facebook @NgrSenate
Asali: Facebook

“Yanzu maganar da na ke yi, gwamnonin APC ba su tare da su. Dalilin shi ne tsohon shugaban jam’iyyar da aka samu matsala da shi, ya taba zama Gwamna.”

Za a samu sauyi wannan karo

Tun da aka kafa jam’iyyar APC a 2014, tsofaffin gwamnoni ne suke shugabancinta, daga Bisi Akande, John Oyegun zuwa Adams Oshiomhole da aka sauke a 2020.

Vanguard ta ce wannan karo ana neman ‘dan takarar da bai shahara sosai ba, da zai jagoranci APC, wannan ne ya sa kusoshin jam’iyyar suka natsu da wannan Sanata.

Yayin da ake shirin zaben 2021 a jihar Anambra, kun ji cewa wani ‘dan takara a PDP ya yi karar hukumar INEC, da Uche Secondus da wasunsu kan hana shi shiga zaben.

Zeribe Ezeanuna ya na kukan ana neman haramta masa takara da wasu kudi da aka kawo a PDP. Lauyansa ya bukaci kotu ta ce a biya shi Naira miliyan 200 ko ya rage zafi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng