Yanzun nan: Motocin mutane sun soye a titi yayin da katuwar motar mai ta fadi a Legas

Yanzun nan: Motocin mutane sun soye a titi yayin da katuwar motar mai ta fadi a Legas

  • Mummunar gobara ta barke a kan titin Legas zuwa Garin Ibadan da safen nan
  • Wata mota da ta dauko kayan man fetur ta fadi, sannan ta kama da wuta a Ogere
  • Ana zargin cewa motoci da sauran abubuwa da dama sun kone a dalilin wutan

Abubuwan hawa da dama suka kone bayan wata mota da ta dauko fetur ta kama ci da wuta a garin Legas, Daily Trust ta fitar da wannan rahoto.

Jaridar ta ce wannan mummunan lamari ya auku ne a daidai sashen Ogere da ke kan babban hanyar Legas zuwa garin Ibadan, jihar Oyo, yau da safe.

Har yanzu ba a tantance adadin mutanen da aka rasa ba, amma wutan ya yi barna sosai. Hakan kuma ya jawo matafiya suka yi carko-carko a titi.

KU KARANTA: Ma’aikacin NDLEA ya hada-kai da wasu, suna cinikin hodar iblis

Wannan babbar hanyar ce ta hada Legas da sauran jihohi, hakan ya sa motoci suke yawan binta. Premium Times ta ce a bara irin haka ya kona motoci 29.

Kokarin da hukumomi su ke yi

Rahoton ya ce ‘yan kwana-kwana suna wurin yanzu haka, suna kokarin kashe wannan gobara, haka zalika ma’aikatan hanya na FRSC sun isa wurin.

Babban jami’in hukumar FRSC na reshen jihar Ogun, Mista Ahmed Umar, ya ce an tado tawaga daga yankin Sahamu zuwa Ogere domin su kawo dauki.

“Wutar ba ta wasa ba ce, amma ba za a iya bayyana adadin motocin da abin ya shafa ba.” Inji Umar.

KU KARANTA: Rundunar Sojoji sun kashe Jagoran ISWAP, Amir Kanemi

Titin Legas-Ibadan
Hanyar Legas zuwa Ibadan Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

“An tuntubi malaman kashe gobara na jihar Ogun, kuma sun iso wurin da abin ya auku. Jami’an FRSC suna yankin, suna ba motocin da suka zo hannu.”

Direbobi suna ta canza hanyar-bi

Direbobi da suka kama hanya zuwa yankin Ogere, suna ta canza hannu, suna bi ta hanyar zuwa sabuwar kasuwar Kara ta Ibadan domin gujewa lamarin.

Hukumar TRACE mai kula da bada hannu a jihar Legas ta ba matafiya shawara su koma bi ta titin Saapade zuwa Ode ko kuma hanyar Remo-Iperu-Sagamu.

A farkon shekarar nan kun ji labari cewa mutum daya ya rasu sakamakon rikicin da ta barke tsakanin Hausawa da Yarbawa a garin Ibadan, a jihar Oyo.

Hakan ya sa aka kone wasu gidajen jama'a, tare da lalata dukiyoyi masu yawa. Jami’an ‘yan sanda da na Amotekun su ka yi kokarin kawo zaman lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel