An kama Ma’aikacin NDLEA a cikin masu laifin saidawa mutane miyagun kwayoyi

An kama Ma’aikacin NDLEA a cikin masu laifin saidawa mutane miyagun kwayoyi

  • Hukumar NDLEA ta kama wasu masu dillancin kwayoyi a jihar Ogun
  • Daga cikin wadanda aka yi ram da su har da wani ma’aikacin NDLEA
  • Jami’an hukumar sun cafke wadannan mutane da hodar iblis da Molly

Hukumar NDLEA da ke da alhakin cafke masu safarar miyagun kwayoyi ta yi ram da wani daga cikin jami’inta mai-ci, a cikin wadanda ke harkar mugayen kwayoyi.

This Day ta rahoto cewa an damke wannan ma’aikaci na hukumar da laifin saida miyagun kwayoyi ga wasu daliban jami’ar tarayya da ‘yan iskan gari a Ogun.

Jaridar ta ce darektan yada labarai da wayar da kai na hukumar ta kasa, Femi Babafemi, ya bayyana haka a wani jawabi da ya fitar wa manema labarai a Abuja.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya umarci kamfanin MTN su rage farashin hawa gizo

Da yake jawabi a ranar Lahadi, Femi Babafemi, ya shaida wa ‘yan jarida an yi ram da mai taimaka wa mutanen da kwayoyi ne a ranar Laraba, 15 ga watan Yuni, 2021.

Today ng ta ce hakan ya biyo bayan tsawon lokaci da aka dauka ana sa ido a kan matar wannan Bawan Allah, inda ake amfani da shagonta wajen yin aika-aikar.

Yadda lamarin ya faru - Jami'in NDLEA

Babafemi ya ce jami’an NDLEA sun yi ta bin wani ‘dan acaba da yaje shagon mai dakin wannan mutumi a garin Abeokuta, aka kama shi ya saye 1.17gm na kwaya.

“Wannan kafin a cafke asalin wanda ake zargi, wani wanda hukuma ta dade ta na nemansa, sai aka yi ram da shi dauke da miyagun kwayoyi.” Inji Femi Babafemi.

KU KARANTA: Rundunar Sojoji sun yi nasarar hallaka Jagoran ISWAP

Ma’aikatan NDLEA
Jami'an NDLEA a bakin aiki Hoto: www.guardian.ng
Asali: UGC

“Daga cikin abubuwan da aka kama shi da su akwai kwalabe 17, giram 22.26 na Codeine; kwayoyi 230 na tramadol; kwayoyi 61 flunitrazepam da giram 48.16 na moli.”

Hukumar ta cigaba: “Bayan an cafke mutane biyu da ake zargi, sai wasu shugabannin kungiyar ‘daliban jami’a su ka tare ma’aikatan NDLEA da motar aikinsu.”

Bayan sa’o’i ana takkadama, ma’aikatan NDLEA sun yi nasarar kama wanda ake zargi zuwa inda aka tsare shi, sannan an kama wani mai saida kwayoyi a garin Ilorin.

A makon jiya ne aka ji wani jam'in Kungiyar ASUU ya na cewa sun shafe wata da watanni ba a biyan Malamai albashinsu a makarantar UNIJOS da ke jihar Filato ba.

Wani babban jami'in gwamnatin tarayya ya maida martani, ya ce karya ne ace akwai Malamai 1, 000 da aka hana albashin watanni, ya ce su tuntubi ma'aikatan jami'arsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel