Ana makokin mutuwar Shekau, Sojoji sun bindige gawurtaccen Janar din ‘Yan Boko Haram

Ana makokin mutuwar Shekau, Sojoji sun bindige gawurtaccen Janar din ‘Yan Boko Haram

  • Boko Haram ba ta gama makokin Shekau ba, sai aka ji Amir Kanemi ya hallaka
  • Sojojin Najeriya sun kai hari, sun kashe Jagoran na Mayakan ta’addan ISWAP
  • Rahotanni sun ce Kanemi ya mutu sakamakon harbi da ya sha a tunbi da cinya

A wani hari da dakarun Operation Hadin Kai na sojoji suka kai a karshen mako, sun hallaka daya daga cikin manyan sojojin kungiyar ta’addan ISWAP.

A ranar Litinin, 21 ga watan Yuni, 2021, jaridar PR Nigeria ta fitar da rahoto cewa an kashe jagora, Amir Kennami wanda aka fi sani da Janar mai ido daya.

Amir Kanemi ya gamu da ajalinsa

Rahotanni sun ce wannan gawurtaccen ‘dan ta’adda ya mutu ne a sakamakon raunin da ya samu daga wani harbin da aka yi masa a yankin tafkin Chadi.

KU KARANTA: Sojoji sun gwabza da 'Yan ta'addan ISWAP a Borno

PR Nigeria ta ce dakarun sojoji na musamman na 134 a karkashin jagorancin Laftanan-Kanal Ishaya Aliyu Manga suka auka wa ‘yan ta’addan ISWAP.

Ishaya Aliyu Manga da sojojinsa sun kashe ‘yan ta’adda a hanyar Gubio zuwa garin Magumeri.

Daily Nigerian take cewa mayakan ‘yan ta’addan na kungiyar ISWAP da dama sun mutu a harin, yayin da Amir Kanemi ya tsere da rauni a cinya da cikinsa.

Daga baya jagoran na kungiyar ISWAP ya mutu a sanadiyyar mummunan raunin da aka yi masa. Sojojinsa sun masa sallah, aka birne shi a boye a Gudumbali.

Ta’adin da Amir Kanemi ya rika yi

Kafin mutuwarsa, Amir Kanemi ya na cikin manyan mayakan ‘yan taddan. A karkashinsa ne Ba-Lawan, Modu Sulum da Amir Modu Borzogo duk suke aiki.

KU KARANTA: Sojoji sun yi wa 'Yan ta'adda barin wuta

Sojoji
Sojojin Najeriya a fagen fama Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Wani jami’in tsaro ya shaida wa ‘yan jarida cewa marigayin ne ya addabi yankunan Magumeri, Nganzai da Gubio, har suka rika kai wa dakarun sojoji hari.

Janar din mai ido daya ya hallaka dinbin mutane a kauyukan Lamisuri, Bijur, Dalari, Bugadam, Talala, Ajigin, Mungusum Gwagwari, Abulam, Ajigin da Doksa.

A ‘yan shekarun nan, marigayin ya kashe mutane a Borgozo, Alagarno, Goniri Marguba da wasu kauyuka irinsu Jewu Lamboa, Limlim a jihohin Borno da Yobe.

Kafin yanzu, an ji an kai wa wa dakarun ISWAP mummunan farmaki, an kuma hallaka manyan Sojojinsu, mai magana madadin rundanar NAF ya bayyana haka.

Bayan an ba Sojoji umarnin hana ‘Yan ta’adda sakat, sun lallasa wasu Dakarun ISWAP a Borno.

Asali: Legit.ng

Online view pixel