Akinwunmi Adesina ya sake zama shugaban AfDB
An sake zaben Dakta Akinwunmi Adesina a matsayin shugaban bankin cigaban nahiyar Afrika, AfDB.
Kwamitin gwamnonin bankin ne suka sake zaben Adesina karo na biyu yayin taron da suka gudanar ta hanyar fasahar intanet a ranar Alhamis a Abidjan.
Hadimar shugaba Muhammadu Buhari, Lauretta Onochie ta tabbatar da zaben a shafin ta na Twitter inda ta wallafa sakon taya Adesina murna.
DUBA WANNAN: An naɗa ɗan Najeriya Ministan Shari'a a Canada (Hotuna)
Onochie ta rubuta, "An sake zaben Akinwunmi Adesina namu a matsayin shugaban bankin cigaban nahiyar Afrika.
"Muna godiya ga shugaban kasar Muhammadu Buhari da ya mara wa Adesina baya, wannan na nuna cewa Adesina ya kere tsaransa."
Wata kwamitin bincike da aka kafa a AfDB ta wanke Adesina daga duk wani zargi na aikata ba dai dai ba.
An kafa kwamitin binciken ne bayan da kasar Amurka ta shigar da korafi a kansa.
Kwamitin ta yi nazarin dukkan zargin da aka masa kuma ta gano babu wani laifi da ya aikata hakan yasa ta yi watsi da shi.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng