ASUU: Gwamnatin Tarayya ta yi wa Malaman Jami’a da ke shirin komawa yajin-aiki raddi

ASUU: Gwamnatin Tarayya ta yi wa Malaman Jami’a da ke shirin komawa yajin-aiki raddi

  • Kungiyar ASUU ta reshen Jami’ar UNIJOS ta ce an hana ‘Ya ‘yanta hakkokinsu
  • Malaman jami’ar Jos suna zargin Gwamnatin Tarayya ta ki biyansu albashinsu
  • Wani jami’in Gwamnati ya ce babu wani malamin jami’a da aka hana hakkinsa

Sabanin gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami’a na kungiyar ASUU ya dauki wani mataki, ofishin akawun gwamnati ya fito ya yi martani.

Jaridar The Nation ta fitar da rahoto a ranar Litinin cewa ofishin akawun gwamnatin tarayya na OAGF, ya musanya zargin da wasu malaman jami’ar suke yi.

Kungiyar ASUU ta reshen UNIJOS ta ce akwai sama da ‘ya ‘yanta 1, 000 da ke koyarwa a jami’ar da suke bin gwamnati bashin albashin watanni biyu zuwa 16.

KU KARANTA: Za mu iya sake shiga wani yajin - aiki - ASUU

Wani jami’in gwamnatin tarayya ya ce babu wasu malamai da aka hana hakkin gumin da su ka yi.

Raddin ofishin Akawun gwamnatin tarayya

Da jaridar ta tuntubi darektan da ya ke kula da manhajar IPPIS na biyan albashi a ofishin babban akawu na kasa, Mista Ben Nsikak, ya ce zargin ba gaskiya ba ne.

Nsikak ya ce babu wani malami da aka yi watanni 13 ba a biya albashinsa. Jami’in ya aika wa ‘yan jarida sako a ranar Asabar, ya ce malaman su tuntubi jami’arsu.

“Ba gaskiya ba ne.”

KU KARANTA: Malaman jami'a suna barazanar shiga sabon yajin-aiki

AGF Ahmed Idris
Akanta-Janar na kasa, Ahmed Idris Hoto: www.thisdaylive.com
Asali: UGC

"Zargin ba a biya malamai sama da 1, 000 da ke karkashin kungiyar ASUU albashin watanni 13, ba gaskiya ba ne.”

“Ana biyan albashi a duk lokacin da ya kamata, kuma ofishin OAGF ba zai hana malaman jami’ar UNIJOS albashin watanni 13, sannan a rika biyan sauran malamai ba."

“Idan har akwai wata matsala, kungiyar ASUU na reshen UNIJOS ya tuntubi OAGF ta hannun ma’ajin makarantarsu domin a warware matsalar.” Inji Ben Nsikak.

Dazu kun samu rahoto cewa matakin haramta Twitter a Najeriya ya jawo an maka Gwamnatin Muhammadu Buhari a gaban wani kotun tarayya da ke garin Abuja.

Kungiyar SERAP ta ce bai dace Gwamnatin Tarayya ta hana mutane aiki da Twitter ba. A dalilin wannan ne kungiyar ta kai karar gwamnati, Ministan labarai da NBC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng