Buhari ya bayyana yadda ya hada doguwar alaka da Bare-bare yayin da ya ziyarci Maiduguri

Buhari ya bayyana yadda ya hada doguwar alaka da Bare-bare yayin da ya ziyarci Maiduguri

  • A ranar Alhamis Muhammadu Buhari ya ziyarci garin Maiduguri, jihar Borno
  • Shugaban kasar ya yi bayanin dangantakarsa da Barebari a fadar Shehun Borno
  • Shugaba Buhari ya tabbatar da cewa akwai mutanen Borno a cikin kakanninsa

Premium Times ta ce a ranar Alhamis, 17 ga watan Yuni, 2021, shugaba Muhammadu Buhari ya yi karin haske game da inda kakanninsa da mahaifansa su ka fito.

Shugaban Najeriyar ya yi wannan magana ne yayin da ya kai ziyara zuwa fadar Mai martaba Shehun Borno, a ranar da ya kaddamar da ayyuka a Maiduguri.

Muhammadu Buhari yake cewa ko da yake shi Bafullatani ne, yana da alaka da kasar Barebari.

KU KARANTA: Ba zan runtsa ba sai 'yan gudun hijira sun koma gida - Buhari

Bayan gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum da Shehun Borno, Abubakar Ibn Umar Garbai El-Kanemi sun kammala jawabi, sai Buhari ya dauko tarihi.

An yi tunanin Mai girma Muhammadu Buhari zai maida martani ne kan jawabin da manyan na kasar Borno su ka yi, amma sai aka ji ya kama wani layin na dabam.

Head Topic ta rahoto Muhammadu Buhari ya na cewa wani bangare na iyayen mahaifiyarsa sun fito ne daga kasar Borno, hakan ya sa yake da dangantaka da jihar.

Alakar Buhari da mutanen kasar Borno

“Zuwa na fadar nan yana da muhimmanci a wuri na; saboda ya tuna mani da asali na ta wurin uwa ta.”
Buhari ya ziyarci Maiduguri
Buhari a Borno Hoto: www.bbc.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Sabon Shugaban EFCC, Bawa ya yi kwanaki 100 a ofis

“Ni din ruwa da yawa ne saboda mahaifiyata dai rabi Hausa ce, rabi kuma Babarbariya. Mahaifina cikakken Bafullatani ne, dari-bisa-dari. Shiyasa nake fada da kowa”

“Mukamin farko da na rike a gidan soja a nan ne, a matsayin gwamnan soji, ina tunanin watanni bakwai rak nayi. Daga baya na zama Ministan mai a gwamnatin Janar Obasanjo.”

Tarihi ya nuna cikin iyayen mahafiyar Buhari, Zulaihat, akwai wadanda mutanen garin Kukawa. Ta bangaren mahaifinsa kuwa, sun tare ne a kasar Daura da su ka zo Najeriya.

Dazu kun samu rahoto cewa Mai magana da yawun Shugaban kasa Muhammaduu Buhari, Malam Garba Shehu, ya yi kaca-kaca da Gwamnonin jihohin adawa na PDP.

Garba Shehu ya ce Gwamnonin PDP ba su tsinana wani aikin fari wajen kawo zaman lafiya da cigaban tattalin arziki sai haddasa fitina a kasar nan ta hanyar yada karyayyaki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel